Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Janye - Tana nufin jan abu daga muhallinsa. Misali; An janye motar da ta lalace ta tare hanyar wucewa. ENG; Drag Away (A turance tana nufin janye)
Jaraba - Tana nufin jin so mai tsanani. Misali; Shan giya ya zama jaraba gare shi, sai ya sha yake jin daɗi. ENG; Excessive Desire (A turance tana nufin jaraba)
Jarfa - Tana nufin tsagun fuska. Misali; Jarfa, gadon gidansu ne. ENG; Facial Markings (A turance tana nufin jarfa)
Jarida - Tana nufi takarda mai ƙunshe da rubutun labarai. Misali; Dattijai na son karanta jarida don jin halin da duniya take ciki. ENG; Newspaper (A turance tana nufin jarida)
Jarirai - Tana nufin jam'in jariri. Misali; Kayan da gwamnati ta kawo na tallafin jarirai ne. ENG; Infants (A turance tana nufin jarirai)
Jariri - Tana nufin wanda ba a daɗe da haifa ba. Misali; An tsinci jariri a unguwarmu. ENG; Infant (A turance tana nufin jariri)
Jarrabawa - Tana nufin gwaji. Misali; Suna gama jarrabawa za a ba su hutu. ENG; Examination (A turance tana nufin jarrabawa)
Jarumi - Tana nufin ƙaƙƙarfa ko jajirtacce. Misali; Shi kaɗai ne jarumi a cikin gidan. ENG; Brave (A turance tana nufin jarumi)
Jauje - Tana nufin abin kiɗa mai kama da kalangu. Misali; A cikin kayan da suke kaɗawa har da jauje. ENG; Drum similar to but larger than kalangu (A turance tana nufin jauje)
Jawabi - Tana nufin bayani a kan wani maudu'i. Misali; A halin yanzu mai girma gwamna ne yake jawabi a ɗakin taron. ENG; Speech (A turance tana nufin jawabi)
1 175 176 177 178 179 337