Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jalla - Tana nufin Allah maɗaukakin sarki.
Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau.
ENG; God (A turance tana nufin jalla)
Jallo - Tana nufin mazubin ruwa na duma.
Misali; Jauro ya shanye ruwan cikin jallo na, sai na ɗebo wani.
ENG; Gourd Water Bottle (A turance tana nufin jallo)
Jam’i - Tana nufin haɗuwar mutane don yin sallah.
Misali; Sun yi jam'i za su yi sallar azahar.
ENG; Congregation of people for joint prayer (A turance tana nufin jam'i)
Jam’iyya - Tana nufin zauren siyasa.
Misali; Dukkansu 'yan jam'iyya ɗaya ne.
ENG; Political Party (A turance tana nufin jam'iyya)
Jama’a - Tana nufin mutane da yawa.
Misali; Bikin ya tara jama'a daga sassan duniya daban-daban.
ENG; The Public (A turance tana nufin jama'a)
Jambaɗe - Tana nufin ƙurajen da ke fitowa a hammata masu zafi sosai.
Misali; Jambaɗe ne ya fito mata kuma ya zuba mata zazzaɓi mai zafi.
ENG; Abscess under armpit (A turance tana nufin jambaɗe)
Jamfa - Tana nufin rigar da ake sa wa a ƙasa kafin a ɗora babbar riga.
Misali; Ya sa jamfa mai gajeren hannu kalar makuba.
ENG; Long sleeve worn as inner garment (A turance tana nufin jamfa)
Jamhuriya - Tana nufin ƙasar da ke da tsarin mulki na musamman.
Misali; Jamhuriyar Niger ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar.
ENG; Republic (A turance tana nufin jamhuriya)
Jami’a - Tana nufin makarantar gaba da sakandire.
Misali; Gambo ya shiga jami'a ne a shekarar da ta gabata.
ENG; University (A turance tana nufin jami'a)
Jami’i - Ma'aikaci, musamman na gwamnati ko wata masana'anta da ya samu horo