Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Jan-baki - Tana nufin abin shafawa a leɓe mai canja masa launi wanda mata ke amfani da shi. Misali; Amaryar ta sha ado da jan-baki. ENG; Lipstick (A turance tana nufin jan-baki)
Jan-gwada - Tana nufin namijin ƙadangare. Misali; Jan-gwada ne ya hana sauran ƙadangarun cin abinci. ENG; Orange-headed male lizard (A turance tana nufin jan-gwada)
Jana’iza - Tana nufin sallar da ake yi wa mamaci kafin a kai shi kabari. Misali; Za a yi jana'iza a babban masallacin Juma'a yau. ENG; Funeral (A turance tana nufin jana'iza)
Janaba - Tana nufin rashin tsarki a addinin musulunci sakamakon biƙi, haila, kusantar iyali da sauransu. Misali; idan mutum na da janaba, ba zai yi sallah ba dole sai ya yi tsarki. ENG; Religious Impurity (A turance tana nufin janaba) Kishiyarta; Tsarki
Janairu - Watan farko ne a shekara. Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu. ENG; January (A turance yana nufin watan farko a shekara)  
Janar - Tana nufin babban muƙamin soja. Misali; Ya kai matakin Janar a aikin soja yanzu. ENG; General (A turance tana nufin janar)
Janareto - Tana nufin injin da ke bayar da wutar lantarki idan an sa masa fetur. Misali; Rashin wuta ya sa janareto ya yi tsada matuƙa. ENG; Generator (A turance tana nufin janareto)
Jangali - Tana nufin kuɗin harajin da ake biyawa shanu. Misali; Malam Modibbo ya biya jangali da wuri wannan karon. ENG; Cattle Tax (A turance tana nufin jangali)
Janjani - Tana nufin ɗaukan lokaci wajen cin abinci, wato ci a hankali a hankali. Misali; Abdulhakim ya fiya janjani. ENG; Slowness in Eating (A turance tana nufin janjani)
January - A turance yana nufin watan farko a shekara. Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu. HAU; Janairu (Watan farko ne a shekara)  
1 174 175 176 177 178 337