Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Babur - Abin hawa ne mai ƙafa biyu. Misali; A kan babur na zo makaranta yau. ENG; Motorcycle (A turance yana nufin babur)
Back - A turance tana nufin baya. Misali; Na goya jariri a baya na. Kishiyarta; Gaba HAU; Baya (Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jiki)
Bad smell - A turance tana  nufin bashi. Misali; Kayan wankin bashi suke saboda ba su sha rana ba. HAU; Bashi (Tana nufin wari mara daɗi)
Baffa - Yana nufin ɗanuwan mahaifi. Misali; Alhaji Barau baffana ne. ENG; Paternal Uncle (A turance yana nufin Baffa)
Bahago - Yana nufin wanda yake amfani da hannun hagu ko kuma mutum mai wuyar sha'ani. Misali; Ado bahago ne. ENG; Left handed person (A turance yana nufin bahago)
Baiko - Yana nufin yarjejeniya tsakanin iyaye don aurar da 'ya'yansu. Misali; Jiya aka yi baikon Abdullahi da Amina. ENG; Bethrothal (A turance yana nufin baiko)
Baiwa - Tana nufin wani abu na musamman da Allah yake ba wa bayinsa wanda ya bambanta su da sauran mutane. Misali; Yaran aji ɗaya suna da baiwa ta musamman, don suna saurin gane karatu. ENG; Gift from God (A turance tana nufin baiwa)
Baki - Gaɓa ce da ke fuskar mutum wadda ake amfani da ita wajen magana, cin abinci da sauransu. Misali; Ya buɗe baki za yi magana sai ruwa ya sakko. ENG; Mouth (A turance yana nufin baki)
Bala’i - Tana nufin faruwar abubuwan tashin hankali da firgici. Misali; Ƙasashen yamma na cikin bala'i saboda afkuwar yaƙe-yaƙe. ENG; Calamity (A turance yana nufin bala'i)
Balaga - Tana nufin matakin girma da mace ko namiji ke kai wa, wanda yake zuwa da canje-canje a halitta da ɗabi'u. Misali; Idan yara sun balaga halayensu kan canja kuma iyaye sai sun dage matuƙa wajen tarbiyya a wannan lokacin. ENG; Puberty (A turance tana nufin balaga)
1 14 15 16 17 18 127