Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Aya - Alama ce ta dakatawa a cikin rubutu.  Misali; Aya alama ce da ke nuna jimla ta zo ƙarshe. ENG; Full stop (A turance tana nufin aya)
Ayaba - Ayaba na daya daga cikin kayan marmari wacce take da matukar amfani ga lafiyar dan adam. Jam'i : Ayaba.
Ayaba - Ɗaya ce daga cikin kayan marmari. Misali; Biri yana son ayaba sosai. ENG; Banana (A turance tana nufin ayaba)
Azumi - Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.  Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu. ENG; Fasting (A turance yana nufin azumi)
Ba’a - Tana nufin aibata mutum ko wata gaɓa ko wani sashe na halittarsa. Misali; Lado ya yi wa Kande ba'a, ya ce mata mai ƙaton hanci. ENG; Mockery (A turance yana nufin ba'a)
Baba - Tana nufin mahaifi. Misali; Baba yana da jikoki arba'in a yanzu. ENG; Father (A turance tana nufin mahaifi)
Babba - Tana nufin abu mai girma. Misali; Gidan da muka siya babba ne. ENG; Big (A turance tana nufin babba) Kishiyarta; Ƙarami
Babban Bankin Najeriya/Babban Bankin Ƙasa - Central Bank of Nigeria (CBN)
Babban Kwamitin ‘Ƴangudun Hijira Na Majalisar Ɗinkin Duniya - United Nations High Commission for Refugees (UNHCR)
Babban Ɗakin Karatu Na Najeriya - National Library Of Nigeria (NLN)
1 16 17 18 19 20 271