Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Barka - Tana nufin gaisuwa. Misali; Ina yi muku barka da yamma. ENG; Greeting (A turance tana nufin barka)
Barkono - Yana nufin tsiro daga cikin kayan lambu, yana kama da tattasai amma shi dogo ne. Misali; Inna ta siyo barkono za ta daka yajin daddawa. ENG; Pepper (A turance yana nufin barkono)
Barrack - A turance tana nufin bariki. Misali; Da na je bariki, na tarar sojoji na atisaye. HAU; Bariki (Tana nufin mazaunin ma'aikata masu ɗamara kamar sojoji da 'yan sanda)
Bashi - Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya. Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa. ENG; Debt (A turance tana nufin bashi)
Bashi - Tana nufin wari mara daɗi. Misali; Kayan wankin bashi suke saboda ba su sha rana ba. ENG; Bad smell (A turance tana  nufin bashi)
Basilla - Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu. Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana. ENG; Large needle (A turance tana nufin basilla)
Batsa - Tana nufin zantuttuka na rashin  ɗa'a. Misali; Wasu daga cikin masu amfani da manhajar TikTok na yawan yin batsa a bidiyoyinsu. ENG; Indecent talk (A turance tana nufin batsa)
Batu - Tana nufin zantuka ko maganganu. Misali; A taron an tattauna batu mai amfani. ENG; Speech ( A turance tana nufin batu)
Bature - Tana nufin mutum farar fata wanda ya zo daga Turai. Misali; Mr. Mike baturen Ingila ne. ENG; European (A turance tana nufin bature)
Bauta - Tana nufin sadaukarwa da biyayya ga abinda mutum ya yarda da shi. Misali; Musulmai sun yarda da Allah shi ne kaɗai abin bauta. ENG; Worship (A turance tana nufin bauta)
1 18 19 20 21 22 127