Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Asusun Tallafawa llimi - Education Trust Funds (ETF)
Atini - Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa. Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi. ENG; Dysentary (A turance yana nufin atini)
Attajiri - Mutum mai tarin dukiya. Misali; Maƙocinmu attajiri ne. Kishiyarta; Talaka ENG; Wealthy person (A turance yana nufin mutum mai dukiya)
Attend - A turance tana nufin halarta. Misali; Taron da aka gabatar a makon da ya gabata, mutane da dama sun halarta. HAU; Halarta (Tana nufin samun damar zuwa gurin da aka gayyaci mutum)
Auduga - Tana nufin tsiro da ake shukawa a gona, ana amfani da ita wajen yin zare da tufafi da sauransu. Misali; Akwai gonakin auduga da yawa a garinmu. ENG; Cotton (A turance tana nufin auduga)
August - A turance yana nufin wata na takwas a shekara Misali; Ɗalibai kan yi hutu a watan Agustan kowacce shekara. HAU; Agusta (Wata ne na takwas a shekara)
Auto Spare Parts Machinery Dealers Association (ASPAMDA) - Ƙungiyar Dilolin injina da kayan Gyara Ta Najeriya
Auto Spare Parts Machinery Dealers Association (ASPAMDA) - Ƙungiyar Dilolin injina da kayan Gyara Ta Najeriya
Awaki - Jam'in akuya. Misali; Kaka yana kiwon awaki. ENG; Goats (A turance tana nufin jam'in akuya)
Axe - A turance tana nufin gatari. Misali; Icen ba zai fasu ba sai an sa gatari. HAU; Gatari (Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen saran itace)
1 15 16 17 18 19 271