Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Babba - Tana nufin abu mai girma. Misali; Gidan da muka siya babba ne. ENG; Big (A turance tana nufin babba) Kishiyarta; Ƙarami
Babban Bankin Najeriya/Babban Bankin Ƙasa - Central Bank of Nigeria (CBN)
Babban Kwamitin ‘Ƴangudun Hijira Na Majalisar Ɗinkin Duniya - United Nations High Commission for Refugees (UNHCR)
Babban Ɗakin Karatu Na Najeriya - National Library Of Nigeria (NLN)
Babbar Cibiyar Horarwa da Binciken Lafiya - Institute of Advanced Medical Research & Training (lAMRT)
Babbar Cibiyar Nazarin Al’ummar Afirka - Center for Advanced Studies of Afircan Society (CASAS)
Babbar Cibiyar Nazarin Shari’a Ta Najeriya - Nigerian Institute of Advanced Legal Studies (NIALS)
Babbar Kotun Ƙasa - Federal High Court
Babbaƙu - Yana nufin baƙaƙen harufan larabci. Misali; Almajiran suna matakin koyon babbaƙu. ENG; Arabic consonants (A turance yana nufin baƙaƙen harufan larabci)
Babu - Tana nufin wayam ko ba komai. Misali; Babu kaya a cikin akwatin. ENG; Without (A turance tana nufin babu)
1 13 14 15 16 17 127