Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Asiri - Tana nufin abinda yake a ɓoye.
Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana satar kayan mutane.
ENG; Secret (A turance tana nufin asiri)
Aski - Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban.
Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa.
ENG; Shaving (A turance yana nufin kwashe gashi)
Assembly - Majalisa, Kungiya
Assembly of Healthcare Professionals Association (AHPA) - Ƙungiyar ƙwararrun malaman lafiya
Asset Management Corporation Of Nigeria (AMCON) - Hukumar kadarori Ta Najeriya
Association - Ƙungiya
Association of Bureau De Change Operators of Nigeria (ABCON) - Ƙungiyar 'yancanji Ta Najeriya
Association for Promoting Nigerian Languages and Culture (APNILAC) - Ƙungiyar Ɗaukaka Al'adu da Harsunan Najeriya
Association of Advertising Agencies of Nigeria (AAAN) - Ƙungiyar kamfanonin Tallace tallace Ta Najeriya
Association of African Universities Agrochemical Producers of Nigeria (AAHAPAN) - Ƙungiyar malaman Dabbobi da maganin feshi Ta Najeriya