Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

April - A turance yana nufin wata na huɗu a shekara.  Misali; Za mu je yawon buɗe ido a watan Afrilu. HAU; Afrilu (A turance yana nufin wata na huɗu a shekara)
Arabic Consonants - A turance yana nufin baƙaƙen harufan larabci. Misali; Almajiran suna matakin koyon babbaƙu. HAU; Babbaƙu (Yana nufin baƙaƙen harufan larabci)
Arabic Script - A turance yana nufin ajami. Misali; Na karanta darasin Ajami a jami'a. ENG; Arabic script (Rubutun Hausa ne amma da harufan larabci)
Aradu - Tsawa da ake yi yayin da ake ruwan sama.  Misali; Mun ji saukar aradu da tsakar dare ana mamakon ruwa. ENG; Thunder (A turance tana nufin tsawa yayin da ake ruwan sama)
Architects Registration Council of Nigeria (ARCON) - Hukumar Ayyukan mazayyana Ta najeriya
Arewa Consuitative Forum (ACF) - Ƙungiyar Tuntubar juna  Ta Arewa
Arewa consultative forum - Gungiyar Tutubar Juna Ta Arewa
Arha - Tana nufin abu mai sauƙin samu, ko kuma wanda ake siyan sa kuɗi kaɗan. Misali; Kayan da Malam yake siyarwa suna da arha. ENG; cheap (A turance tana nufin arha)  
Armpit - A turance tana nufin hammata. MIsali; An ce goga alimun a hammata yana hana warin jiki. HAU; Hammata (Tana nufin gaɓar ƙarƙashin hannu)
Arne - Tana nufin wanda ba shi da addini.  Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne. ENG; Pagan (A turance tana nufin arne)
1 10 11 12 13 14 269