Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ambush - A turance tana nufin fako. Misali; Shi suke fako, yana zuwa suka cafke shi. HAU: Fako (Tana nufin ɓuya don kai harin ba-zata)
Amnestic Psychology Association (APA) - Ƙungiyar masana mutuntaka Ta Amurka
Amnesty international (AI) - Hukumar Afuwa Ta Duniya /Hukumar bibiyar Haƙƙi Ta Duniya
Amosani - Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi. Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta. ENG; Dandruff (A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai)
An elder - A turance tana nufin dattijo. Misali; Mahaifinta dattijo ne saboda yana da dattako. HAU; Dattijo (Tana nufin babban mutum mai kima wanda shekarunsa suka ja)
Ango - Wanda aka ɗaurawa aure. Misali; Mukhtar ango ne. Kishiyarta; Amarya ENG; Bride-groom (A turance tana nufin wanda ya yi aure)
Annabi - Wanda Allah ya aiko da saƙon addini. Misali; Shugaban annabawa shi ne annabi Muhammad (S.A.W) ENG; Prophet (A turance yana nufin wanda Allah ya aiko)
Anus - A turance tana nufin dubura. Misali; Dubura ɗaya ce daga cikin gaɓɓan jiki. HAU; Dubura (Tana nufin gaɓar da ake bayan gari da ita (kashi))
Any Lawful Act - A turance tana nufin halal. Misali; Cin naman shanu halal ne a musulunci. HAU; Halal (Tana nufin duk abin da addini ya ba da damar a yi) Kishiyarta; Haram
Any major muslim festival - A turance tana nufin idi. Misali; Yara na matuƙar son idi musamman na sallah babba da ƙarama. HAU; Idi (Tana nufin biki)
1 9 10 11 12 13 298