Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Alhamis - Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako.
Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis.
ENG; Thursday (A turance tana nufin rana ta huɗu a mako)
Alkinta - Dabbobi na gida da ake kiwatawa ko ajiyewa domin ci ko siyarwa, kamar shanu da tumaki da awaki da sauransu.
All Nigerian Conference Of Principals of Secondary School (ANCOPSS) - Ƙungiyar shugabannin makarantun sakandare Ta Najeriya
All Farmers Association of Nigeria (AFAN) - Kadaurar Dukkanin manoma Ta Najeriya
All Local Governments Of Nigeria (AlGON) - Ƙungiyar ƙananan Hukumomi Ta Najeriya
Allo - Abin rubutu ne galibi na katako.
Misali; Malami yana rubutu a kan allo.
ENG; Blackboard (A turance yana nufin allon rubutu)
Almajiri - Yaro ne da yake koyon karatun addini.
Misali; Abbas almajiri ne.
ENG; Pupil/Student (A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani)
Alphabet - A turance tana nufin harafi.
Misali; Ana fara rubuta sunan yanka da babban harafi.
HAU; Harafi (Tana nufin baƙi ko wasalin da ake amfani da su wajen gina kalma)
Alqalami - Alƙalami:abin da ake rubutu da shi.
Jam'i : Alƙalama.
Always - A turance tana nufin jiddin.
Misali; Ai Jiddin yana masallaci tunda Allah ya shirye shi.
HAU; Jiddin (Tana nufin kodayaushe)