Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Agriculture Allied Employees’ Union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar malaman Gona Ta Najeriya
Agriculture Allied Employees’union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar Malaman Gona Ta Najeriya
Agusta - Wata ne na takwas a shekara.
Misali; Ɗalibai kan yi hutu a watan Agustan kowacce shekara.
ENG; August (A turance yana nufin wata na takwas a shekara)
Ahuwa - Yana nufin sassauci ko yafiya.
Misali; An yi wa masu laifin afuwa.
ENG; Liniency/Pardon (A turance yana nufin sassauci ko yafiya)
Aiki - Aiki wani abu ne da mutane suke yi domin dogaro da kai.
Jam'i : Ayyuka.
Aimless Wandering - A turance tana nufin gantali.
Misali; Mijin ya saki matar ne saboda tana da gantali.
HAU; Gantali (Tana nufin tsananin yawo)
Air - A turance tana nufin iska.
Misali; Tun safe iska mai sanyi take kaɗawa yau.
HAU; Iska (Tana nufin abin da ke kaɗawa kuma ababen halitta ke shaƙa don su rayu)
Air Transport Services Senior Staff Association of Nigeria (ATSSSAN) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Sufurin Jirgin Sama Ta Najeriya
Airline Operators of Nigeria (AON) - Ƙungiyar kamfanonin jirgin sama Ta Najeriya
Ajami - Rubutun Hausa ne amma da harufan larabci.
Misali; Na karanta darasin Ajami a jami'a.
ENG; Arabic script (A turance yana nufin ajami)