Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
African women’a Development fund (AWDF) - Asusun kyautata Rayuwar matan Afirka
Afrilu - Wata na huɗu ne a shekara.
Misali; Za mu je yawon buɗe ido a watan Afrilu.
ENG; April (A turance yana nufin wata na huɗu a shekara)
Agaji - Yana nufin taimako.
Misali; Gwamnati ta kai agaji gidan gyaran hali da tarbiyya.
ENG; Help/Assistance (A turance yana nufin taimako)
Agency - Hukuma, Ma'aikata
Agogo - Yana nufin manunin lokaci.
Misali; Na siyo sabon agogo a kasuwa.
ENG; Clock/Watch (A turance yana nufin agogo)
Agola - Yana nufin ɗan da mace ta zo da shi daga gidan tsohon mijinta zuwa gidan sabon mijinta.
Misali; Idi agola ne, mahaifina ne ya auri mahaifiyarsa bayan mahaifinsa ya rasu.
ENG; Step-child (A turance yana nufin agola)
Agricultural Research Council of Nigeria (ARCN) - Hukumar binciken Noma Ta Najeriya
Agriculture Allied Employees’ Union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar malaman Gona Ta Najeriya
Agriculture Allied Employees’union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar Malaman Gona Ta Najeriya
Agusta - Wata ne na takwas a shekara.
Misali; Ɗalibai kan yi hutu a watan Agustan kowacce shekara.
ENG; August (A turance yana nufin wata na takwas a shekara)