Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ahuwa - Yana nufin sassauci ko yafiya. Misali; An yi wa masu laifin afuwa. ENG; Liniency/Pardon (A turance yana nufin sassauci ko yafiya)
Aiki - Aiki wani abu ne da mutane suke yi domin dogaro da kai. Jam'i : Ayyuka.  
Air Transport Services Senior Staff Association of Nigeria (ATSSSAN) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Sufurin Jirgin Sama Ta Najeriya
Airline Operators of Nigeria (AON) - Ƙungiyar kamfanonin jirgin sama Ta Najeriya
Ajami - Rubutun Hausa ne amma da harufan larabci. Misali; Na karanta darasin Ajami a jami'a. ENG; Arabic script (A turance yana nufin ajami)
Akaifa - Yana nufin farce, na yatsun hannu ko ƙafa.  Misali; Na kira mai yankan akaifa zai yanke min yanzu. ENG;Fingernail (A turance yana nufin farce)
Akushi - Mazubin abinci wanda ake yi da katako.  Misali; Binta ta zuba abincin a cikin akushi. ENG;Bowl (A turance yana nufin mazubin abinci na katako)
Akuya - Akuya wata dabba ce wadda take rayuwa cikin mutane a cikin gari,mutane na kiwata ta domin aci a matsayin abinci ko kuma a sayar ayi amfani da kudin. Jam'i : Akuyoyi.
Al’umma - Tana nufin mutane ko jama'ar wani yanki. Misali; Al'ummar Hausawa na da ɗimbin tarihi. ENG; Nation (A turance tana nufin al'umma)
Alayyahu - Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya. Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma. ENG; Spinach (A turance yana nufin ganyen alayyahu)
1 4 5 6 7 8 147