Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Asawaki - Itace ne da ake goge haƙora da shi. Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan. ENG; Chewing stick (A turance yana nufin asawaki)
Ashana - Tana nufin abin kunna wuta.  Misali; Da ashana na kunna wuta na yi girki. ENG; Matches (A turance tana nufin ashana)
Asiri - Tana nufin abinda yake a ɓoye.  Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana  satar kayan mutane. ENG; Secret (A turance tana nufin asiri)
Aski - Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban.  Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa. ENG; Shaving (A turance yana nufin kwashe gashi)
Assembly - Majalisa, Kungiya
Assembly of Healthcare Professionals Association (AHPA) - Ƙungiyar ƙwararrun malaman  lafiya
Asset Management Corporation Of Nigeria (AMCON) - Hukumar kadarori Ta Najeriya
Association - Ƙungiya
Association of Bureau De Change Operators of Nigeria (ABCON) - Ƙungiyar 'yancanji Ta Najeriya
Association for Promoting Nigerian Languages and Culture (APNILAC) - Ƙungiyar Ɗaukaka Al'adu da  Harsunan Najeriya
1 8 9 10 11 12 127