Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Arewa consultative forum - Gungiyar Tutubar Juna Ta Arewa
Arha - Tana nufin abu mai sauƙin samu, ko kuma wanda ake siyan sa kuɗi kaɗan.
Misali; Kayan da Malam yake siyarwa suna da arha.
ENG; cheap (A turance tana nufin arha)
Armpit - A turance tana nufin hammata.
MIsali; An ce goga alimun a hammata yana hana warin jiki.
HAU; Hammata (Tana nufin gaɓar ƙarƙashin hannu)
Arne - Tana nufin wanda ba shi da addini.
Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne.
ENG; Pagan (A turance tana nufin arne)
Arrow - A turance tana nufin kibiya.
Misali; Jarumin ya harba kibiya a ƙirjin dokin.
HAU; Kibiya (Tana nufin abin da ake ƙerawa, ana mafani da ita don yin harbi)
Artifacts Rescuer Association of Nigeria (ARAN) - Ƙungiyar Adana Tarkacen Tarihi Ta najeriya
Asabar - Rana ce ta shida a ranakun mako.
Misali; Ranar Asabar ne bikin.
ENG; Saturday (A turance tana nufin rana ta shida a mako)
Asali - Tana nufin tushe ko mafari.
Misali; Annabi Muhammad yana da kyakkyawan asali.
ENG; Origin (A turance tana nufin asali)
Asawaki - Itace ne da ake goge haƙora da shi.
Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan.
ENG; Chewing stick (A turance yana nufin asawaki)
Ashana - Tana nufin abin kunna wuta.
Misali; Da ashana na kunna wuta na yi girki.
ENG; Matches (A turance tana nufin ashana)