Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Haƙilo - Tana nufin yin abu da gaske ka'in da na'in, tare da kai komo.
Misali; Ɗaliban na ta haƙilo don ganin ba su faɗi jarrabawa ba.
ENG; Giving much effort for little gain (A turance tana nufin haƙilo)
Haƙori - Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam da sauran halittu, wanda ake amfani da shi wajen tauna.
Misali; Ba zai iya tauna ƙashi ba saboda ba shi da haƙori.
ENG: Tooth (A turance tana nufin haƙori)
Haƙuri - Tana nufin dangana da rashin ɗaukar mataki idan an maka laifi.
Misali; Ya samu mace mai haƙuri shi yasa zamansu ya yi tsayi.
ENG; Patience (A turance tana nufin haƙuri)
Kishiyarta; Rashin haƙuri
He-goat - A turance tana nufin bunsuru.
Misali; Malam Rabi'u ya siyo bunsuru shekaran jiya.
Kishiyarta; Akuya
HAU; Bunsuru (Tana nufin namijin akuya.)
Head Pad - A turance tana nufin gammo.
Misali; Ka sa gammo a kanka saboda kayan na da nauyi.
HAU; Gammo (Tana nufin tsumman da ake nannaɗawa a sa a saman kai idan za a ɗauki kaya)
Head-tie - A turance yana nufin maɗaurin kai na mata.
Misali; Kande ta ɗaure kai da adiko.
HAU; Adiko (Maɗaurin kai na mata)
Heads - A turance tana nufin kawuna.
Misali; 'Yan gidan manyan kawuna garesu.
HAU; Kawuna (Tana nufin jam'in kai)
Heads of State & Government of the Niger Basin Authority - Kadaurar Shugabannin Ƙasashe da Gwanmnatoci Mamallakar Kogin Kwara
Help - A turance tana nufin gudunmawa.
Misali; Gwamnati ta kawo gudunmawa ga waɗanda ibtila'in gobara ya afkawa.
HAU; Gudunmawa (Tana nufin tallafi ko agaji)
Help/Assistance - A turance yana nufin taimako.
Misali; Gwamnati ta kai agaji gidan gyaran hali da tarbiyya.
HAU; Agaji (Yana nufin taimako)