Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
United Nations Industrial Development Organization (UNICEF) - Hukumar Bunƙasa Masana'antu Na Majilisar Ɗinkin Duniya
United Nations International Children’s Emergency Fund (UNICEF) - Hukumar Kyautata Rayuwar Yara Ta Majilisar Ɗinkin Duniya
United States Agency for International Development (USAID) - Hukumar Bunƙasa Ƙasashe Masu Tasowa Ta Ƙasar Amurka
Universal Basic Education Commission (UBEC) - Hukumar llimin Baiɗaya
Upper Benue River Basin Development Authority (UBRBDA) - Hukumar Bunƙasa Yankunan Kogin Binuwai
Uproot - A turance tana nufin ɓaɓɓake.
Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa.
HAU; Ɓaɓɓake (Tana nufin jijjige abu daga tushensa)
Urine - A turance yana nufin bawali.
Misali; Ya yi bawali a ƙofar makaranta.
HAU; Bawali (Tana nufin fitsari)
Uwar Garke - Babbar ƙafa ko garken da yake ba wa sauran kafafen intanet damar shige da fice domin samun bayani.
Uwar Kudi - Jari ko tsagwaron kudin da ake juyawa a harkar kasuwanci.
Veterinary Conucil of Nigeria (VCN) - Majalisar Likitocin Dabbobi Ta Najeriya