Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hatsi - Tana nufin tsabar abinci kamar gero, masara, dawa da sauransu.
Misali; Akwai rumbun hatsi a gidan maigari.
ENG; Grain (A turance tana nufin hatsi)
Haughtiness - A turance tana nufin izza.
Misali; Sarautar da aka naɗa shi ta sa shi jin izza.
HAU; Izza (Tana nufin jin isa da faɗin rai)
Hauka - Tana nufin rashin ciwon rashin hankali ko gushewar hankali.
Misali; Ya shekara goma yana fama da ciwon hauka.
ENG; Madness (A turance tana nufin hauka)
Kishiyarta; Hankali
Hauni - Tana nufin mai yanke hukuncin kisa.
Misali; Ɓarayin sun gamu da hauni a kotu.
ENG; Executioner (A turance tana nufin hauni)
Haure - Tana nufin haƙori.
Misali; Da hauren giwa ake haɗa maganin.
ENG; Tusk (A turance tana nufin haure)
Hausa person who has no Fulani ancestry - A turance tana nufin haɓe.
Misali; Abokin Jauro haɓe ne.
HAU; Haɓe (Tana nufin wanda ba bafulatani ba. Fulani kan kira wanda ba ɗan ƙabilarsu ba da wannan suna)
Haushi - Tana nufin kukan kare.
Misali; Tuna farkon dare kare yake ta haushi a waje.
ENG; Barking (A turance tana nufin haushi)
Have as much as one can stand - A turance tana nufin ginsa.
Misali; Cin abinci nau'i ɗaya kullum na da ginsa.
HAU; Ginsa (Tana nufin isa ko fita daga rai)
Hawainiya - Tana nufin wata dabba mai kama da ƙadangare, tana canja launi ta saje da inda take don ba wa kanta kariya daga abokan gaba.
Misali; Hawainiya na tafiya ne a hankali kamar dodon koɗi.
ENG: Chameleon (A turance tana nufin hawainiya)
Hayaƙi - Tana nufin abin da yake fitowa daga wuta idan an kunna, yana cutar da huhu musamman idan ana shaƙar sa da yawa.
Misali; Hayaƙi yana tashi saboda itacen ɗanye ne.
ENG; Smoke (A turance tana nufin hayaƙi)