Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Town - A turance tana nufin birni. Misali; A birni ake samun manyan gidaje da manyan makarantu Kishiyarta; Ƙauye HAU; Birni (Tana nufin maraya ko inda ababben more rayuwa na zamani suke)
Town Planners Registration Council of Nigeria (TOPREC) - Hukumar Ayyukan Matsara Birane Ta Najeriya
Trade Union Congress of Nigeria (TUC) - Kadaurar Ƙungiyoyin 'Ƴankasuwa Ta Najeriya
Transmission Company of Nigeria (TCN) - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Najeriya
Tree - A turance tana nufin bishiya. Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma. HAU; Bishiya (Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan)
Tribunal - Kotun Wucin Gida
Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Tsagaita - Tsahirtawa daga yin, ko barin wani abu ta hanyar taƙaitawa ko kaucewa, kamar daina yin abin da yake jawo ko haifar da asarar dukiya ko ta rayuwa.
Tsaron Sirri - Aikin tsaro ne da jami'an tsaro na farin kaya suke yi a boye domin nesa daga magauta.
Tuesday - A turance tana nufin rana ta biyu a mako. Misali; Kasuwar tana ci ranar Talata. HAU; Talata (Rana ta biyu a cikin ranakun mako)
1 133 134 135 136 137 144