Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Guinea Corn - A turance tana nufin dawa. Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya. HAU: Dawa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi)
Guinea-worm - A turance tana nufin kurkunu. Misali; An yi nasarar kawar da cutar kurkunu a Najeriya. HAU; Kurkunu (Tana nufin cutar fata mai sanya ƙuraje)
Gujjiya - Tana nufin nau'in abin ci mai kama da wake amma ta fi wake girma, kuma a cikin kwanso take, sai an ɓare. Misali; Ina son gujjiya sosai, na ji an ce har tuwonta ake yi. ENG; Bambara Groundnut (A turance tana nufin gujjiya)
Gulbi - Tana nufin kwari da ruwa yake taruwa. Misali; Indo da ƙawayenta sun tafi gulbi yin wanki. ENG; River (A turance tana nufin gulbi)
Gulma - Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa. Misali; Musulunci ya haramta gulma. ENG; Setting one person against another through gossip (A turance tana nufin gulma)
Gulp, Drink Quickly -

A turance tana nufin kwankwaɗa.

Misali; Ado ya samu ruwan sanyi ya kwankwaɗa bayan sun gama wasan kwallon kafa.

HAU; Kwankwaɗa (Tana nufin shan ruwa ko abin sha cikin sauri)

Gum - A turance tana nufin danƙo. Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa. HAU; Danƙo (Tana nufin abu mai mannewa)
Gum - A turance tana nufin ƙaro. Misali: Ana amfani da ƙaro wajen yin tawadar da ake rubutu. HAU: Ƙaro (Tana nufin wani abu mai ɗanko da ke fitowa  a jikin bishiya).
Gumba - Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa. Misali; An raba gumba a gidan mutuwar. ENG; Sweet pounded millet mixed with water (A turance tana nufin gumba)
Gumi - Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu. Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake. ENG; Sweat (A turance tana nufin gumi)
1 132 133 134 135 136 337