Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Green slime collecting on stagnant water - A turance tana nufin gansakuka. Misali; Bangon duk ya yi gansakuka saboda damina. HAU; Gansakuka(Tana nufin wani koren abu da yake fitowa a guraren da danshi yake)
Greeting - A turance tana nufin barka. Misali; Ina yi muku barka da yamma. HAU; Barka (Tana nufin gaisuwa)
Grey Hair - A turance tana nufin furfura. Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina. HAU; Furfura (Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa)
Grind Coarsely - A turance tana nufin ɓarza. Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma. HAU; Ɓarza (Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba)
Groaning - A turance tana nufin ƙugi. Misali: Ana jin ƙugin cikinsa saboda ciwon da yake masa. HAU: Ƙugi (Tana nufin ƙara)
Ground Squirrel - A turance tana nufin kurege. Misali; Ado ya bi kurege har cikin raminsa ya kamo shi. HAU; Kurege (Tana nufin wata dabba mai kama da zomo)
Groundnut - A turance tana nufin gyaɗa. Misali; Ina son dafaffiyar gyaɗa. HAU; Gyaɗa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abin ci mai ɗauke da sinadaren gina jiki, ana sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban)
Growling - A turance tana nufin gurnani. Misali; Ba zan iya shiga gidan ba, na jiyo kare yana gurnani. HAU; Gurnani (Tana nufin gunji da dabbobi ke yi musamman kare da zaki)
Gruel made of guinea-corn or millet flour - A turance tana nufin kunu. Misali; An dama wa mai jego kunu. HAU; Kunu (Tana nufin abin sha wanda ake yi da gari ko markaɗaɗɗen gero mai ƙunshe da kayan ƙamshi da tsamiya ko kanwa)
Guava - A turance tana nufin goba. Misali; Goba tana da sinadarai masu inganta lafiya a cikinta. HAU; Goba (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari tana da ƙananan ƙwallaye a cikinta)
1 130 131 132 133 134 337