Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hankali - Tana nufin sanin ya kamata.
Misali; Idris yana da hankali da sanin ya kamata.
ENG; Sense (A turance tana nufin hankali)
Kishiyarta: Rashin Hankali
Hankaɗa - Tana nufin turawa da ƙarfi.
Misali; Ya hankaɗa ta ta faɗi ƙasa.
ENG; Push Forward (A turance tana nufin hankaɗa)
Hankici - Tana nufin ƙyallen da ake goge gumi.
Misali; Na goge fuska ta da hankici don na yi gumi da yawa.
ENG; Handkerchief (A turance tana nufin hankici)
Hannu - Tana nufin gaɓa daga cikin gaɓɓan jiki.
Misali; Na wanke hannu zan ci abinci.
ENG; Hand (A turance tana nufin hannu)
Hanta - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ciki wadda ke tace jini da fitar da datti daga cikin jini.
Misali; Farfesun hanta zan dafa a matsayin karin kumallo.
ENG; Liver (A turance tana nufin hanta)
Hantsa - Tana nufin nono ko mama ko tsakiyar wando.
Misali; 1. Hantsar wandons ta yage.
2. Saniyar tana da manyan hantsa.
ENG; Breast/Crotch of trousers (A turance tana nufin hantsa)
Hantsi - Tana nufin lokacin da rana ta fito daga misalin ƙarfe bakwai zuwa sha ɗaya na safe.
Misali; Da hantsi za mu je gidan adana namun daji.
ENG; Time of the day (A turance tana nufin hantsi)
Hanya - Tana nufin guri ko inda ake wucewa.
Misali; Gwamnati ta gina hanya a tsakanin ƙauyukan guda biyu.
ENG; Road/ Path (A turance tana nufin hanya)
Hanzari - Tana nufin sauri ko gaggawa.
Misali; Ku yi hanzari kar ku makara.
ENG; Speed/ Haste (A turance tana nufin hanzari)
Hanƙoro - Tana nufin nuna zaƙuwa.
Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa.
ENG; Showing eagerness (A turance tana nufin hanƙoro)