Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Zayyana - Aikin zana tsari da yadda zubin mahalli, kamar gida zai kasance a gine.
Ɓaci - Tana nufin lalacewa. Misali; Rigar ta ɓaci da amai sai an sake wata. ENG; Spoiled (A turance tana nufin ɓaci)
Ɓagas - Tana nufin samun abu cikin sauƙi ba tare da an sha wahala ba. Misali; A ɓagas y samu kayan da ya siyo. ENG; Cheaply (A turance tana nufin ɓagas)
Ɓararraka - Tana nufin dahuwa ba ƙaƙƙautawa. Misali; Waken yana ta ɓararraka tun ɗazu. ENG;Boil Continuously (A turance tana nufin ɓararraka)
Ɓarawo - Ɓarawo wani mutum ne mai satar kayan da ba nashi ba da niyyar ɗauka babu izini. Jam'i : Ɓarayi
Ɓarawo - Tana nufin mutumin da yake sata. Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare. ENG; Thief (A turance tana nufin ɓarawo)
Ɓargo - Tana nufin abin da yake cikin ƙashi ko laka. Misali; Girkin ya yi daɗi musamman ma ƙashin miyar saboda akwai ɓargo a ciki. ENG; Bone marrow (A turance tana nufin ɓargo)
Ɓari - Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba. Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar. ENG;Dropping Something (A turance tana nufin ɓari)
Ɓari - Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi. Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi. ENG; Shivering (A turance tana nufin ɓari)
Ɓarna - Tana nufin lalata abu. Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai ENG; Damage (A turance tana nufin ɓarna)
1 138 139 140 141 142