Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ɓarawo - Tana nufin mutumin da yake sata.
Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare.
ENG; Thief (A turance tana nufin ɓarawo)
Ɓargo - Tana nufin abin da yake cikin ƙashi ko laka.
Misali; Girkin ya yi daɗi musamman ma ƙashin miyar saboda akwai ɓargo a ciki.
ENG; Bone marrow (A turance tana nufin ɓargo)
Ɓari - Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba.
Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar.
ENG;Dropping Something (A turance tana nufin ɓari)
Ɓari - Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi.
Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi.
ENG; Shivering (A turance tana nufin ɓari)
Ɓarna - Tana nufin lalata abu.
Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai
ENG; Damage (A turance tana nufin ɓarna)
Ɓarza - Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba.
Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma.
ENG; Grind Coarsely (A turance tana nufin ɓarza)
Ɓata - Tana nufin a nemi abu a rasa.
Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba.
ENG; Lost (A turance tana nufin ɓata)
Ɓauna - Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya.
Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi.
ENG; Bush-cow (A turance tana nufin ɓauna)
Ɓaɓatu - Tana nufin magana ba ƙaƙƙautawa.
Misali; Mun baro su suna ta ɓaɓatu a ɗakin taron.
ENG; Noisy (A turance tana nufin ɓaɓatu)
Ɓaɓe - Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa.
Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya.
ENG; Break Off relationship (A turance tana nufin ɓaɓe)