Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Girbi - Tana nufin kwashe amfanin gona bayan ya gama nuna.
Misali; Manoman na cikin farin ciki sakamakon lokacin girbi ya yi.
ENG; Reap (A turance tana nufin girbi)
Girgije - Tana nufin gajimaren da yake ɗauke da ruwa.
Misali; Girgije ya lulluɓe sararin samaniya.
ENG; Rain-Cloud (A turance tana nufin girgije)
Girgiɗe - Tana nufin cire abu da ƙarfi.
Misali; An girgiɗe mata haƙorin don ya ishe ta da ciwo.
ENG; Uproot By Shaking (A turance tana nufin girgiɗe)
Girka - Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta.
Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke.
ENG; Putting a pot on the fire (A turance tana nufin girka)
Girl friend/ Unmarried girl of marriageable age - A turance tana nufin budurwa.
Misali; Fiddausi ta zama budurwa, baɗi za a yi mata aure.
HAU; Budurwa (Tana nufin yarinyar da ta isa aure)
Gishiri - Tana nufin sinadarin da ke ba wa abinci ɗanɗano.
Misali; Kirarinsa shi ne: Gishiri in ba kai ba miya.
ENG: Salt (A turance tana nufin gishiri)
Giving much effort for little gain - A turance tana nufin haƙilo.
Misali; Ɗaliban na ta haƙilo don ganin ba su faɗi jarrabawa ba.
HAU; Haƙilo (Tana nufin yin abu da gaske ka'in da na'in, tare da kai komo)
Giwa - Tana nufin wata dabbar daji mai girma, ita ce mafi gima a cikin dabbobin da suke doron ƙasa.
Misali; Giwa tana da manyan kunnuwa masu faɗi.
ENG; Elephant (A turance tana nufin giwa)
Giya - Tana nufin abin sha mai gusar da hankali.
Misali; Da ya sha giya ya lakaɗa wa matarsa duka sakamakon yana cikin maye.
ENG; Alcoholic Drink (A turance tana nufin giya)
Gizo - Tana nufin ƙwaro mai yin yana a bango, yana da ƙafafu guda takwas.
Misali; Gizo-gizo ya yi yawa a ɗakin.
ENG; Spider (A turance tana nufin gizo)