Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fyaɗe - Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba. Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya. ENG; Rape (A turance tana nufin fyaɗe)
Gaba - Tana nufin daina yi wa juna magana. Misali; Ai sun daɗe suna gaba da juna saboda dalilin da bai kai ya kawo ba. ENG; Enmity (A turance tana nufin gaba)
Gabani - Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki. Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta. ENG; The time just before (A turance tana nufin gabani)
Gado - Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta. Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa. ENG; Bed (A turance tana nufin gado)
Gado - Tana nufin kuɗi da kadarorin da mamaci ke bar wa iyalansa, ma'ana duk abin da mutum ya mallaka idan ya mutu ya zama gado. Misali; Iyalan na rikici akan rabon gado. ENG; Inheritance (A turance tana nufin gado)
Gafaka - Tana nufin jakar fata da ake yi musamman don saka littattafai. Misali; Malamin ya saka Al'ƙur'ani a gafaka. ENG; Satchel (A turance tana nufin gafaka)
Gafara - Tana nufin yafiya musamman ta Allah SWT. Misali; Allah mai gafara ne ga bayinsa. ENG; Pardon/Forgiveness (A turance tana nufin gafara)
Gafiya - Tana nufin ƙaton ɓera. Misali; Ramin gafiya ne a gurin. ENG; Giant Rat (A turance tana nufin gafiya)
Gagarumi - Tana nufin babban abu mai muhimmanci. Misali; Gwamnati ta haɗa gagarumin taron masu sana'o'in gargajiya. ENG; Big/Important (A turance tana nufin gagarumi)
Gaggauta - Tana nufin a yi abu da sauri ko hanzari. Misali; Ku gaggauta gamawa saboda lokacin tashi ya yi. ENG; Hurry (A turance tana nufin gaggauta)
1 116 117 118 119 120 337