Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gayya - Tana nufin taro ko mutane da yawa. Misali; Samarin yankin na yin aikin gayya a kowane mako. ENG; Communal Work (A turance tana nufin gayya)
Gayya - Tana nufin da gangan ko ana sane. Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa. ENG: Things done or said intentionally (A turance tana nufin gayya)
Gayyata - Tana nufin kira zuwa wani sha'ani, wato sanar da mutum cewa ana buƙatar ya zo. Misali; Malaman sun samu saƙon gayyata ne daga hukumar ilimi ta ƙasa. ENG; Invite (A turance tana nufin gayyata)
Gaza - Tana nufin kasawa. Misali; Sakamakon da ya samu ya gaza kai wa yanda za a ɗuake shi a jami'a. ENG; Fail To Do (A turance tana nufin gaza)
Gaɓar Teku - Iyaka ko fadin inda kasa, kamar najeriya take iko da shi a cikin teku.
Gaɗa - Tana nufin tafi da waƙe-waƙe da 'yanmata ke yi musamman a dandali. Misali; 'Yanmatan sun shirya gaɗa saboda murnar bikin ƙawarsu. ENG; Girl's game of clapping and singing (A turance tana nufin gaɗa)
Gefe - Tana nufin wani sashe. Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya. ENG; Side (A turance tana nufin gefe)
Gemu - Tana nufin gashin da yake fitowa a haɓar maza. Misali; Ya aske gemunsa ranar Lahadi. ENG; Beard (A turance tana nufin gemu)
General - A turance tana nufin janar. Misali; Ya kai matakin Janar a aikin soja yanzu. HAU; Janar (Tana nufin babban muƙamin soja)
Generator - A turance tana nufin janareto. Misali; Rashin wuta ya sa janareto ya yi tsada matuƙa. HAU; Janareto (Tana nufin injin da ke bayar da wutar lantarki idan an sa masa fetur)
1 114 115 116 117 118 300