Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gatse - Tana nufin a faɗi abu saɓanin abinda ake nufi.
Misali; Ta yi musu gatse tace su faɗa wuta.
ENG; Sarcasm (A turance tana nufin gatse)
Gauraka - Tana nufin tsuntsu wanda yake rayuwa kusa da fadamu.
Misali; Ana samun tsuntsun gauraka a kudu maso yammacin Afirika.
ENG; Crownbird (A turance tana nufin gauraka)
Gauraya - Tana nufin cakuɗa abubuwa su zama ɗaya.
Misali; Ado ya gauraya garin dawar da rogo.
ENG; Mix Together (A turance tana nufin gauraya)
Gauta - Tana nufin busasshiyar ɗata.
Misali; A cikin maganin sanyin har da gauta.
ENG; Dried form of garden egg (A turance tana nufin gauta)
Gawa - Tana nufi mataccen abu ko abinda ba shi da rai.
Misali; Duk wanda ya shiga yankin da ake yaƙi ya zama gawa.
ENG; Corpse (A turance tana nufin gawa)
Gawurta - Tana nufin shahara ko bunƙasa ko kai wa ƙololuwar matsayi.
Misali; Kamfanin sun gawurta, yanzu sukan fitar da kayayyakinsu zuwa ƙasashen ƙetare.
ENG; Become Great (A turance tana nufin gawurta)
Gaya - Tana nufin ƙololuwa ko ƙarshe.
Misali; Yaran sun yi ƙoƙari matuƙa gaya.
ENG; Extreme End (A turance tana nufin gaya)
Gaya - Tana nufin tsura ko tsirara.
Misali; Ta dama min fura gaya, ba nono bare suga.
ENG; Naked State (A turance tana nufin gaya)
Gayauna - Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma.
Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa.
ENG; Small patch or plot of land given to a young boy to farm on (A turance tana nufin gayauna)
Gaye - Tana nufin matashi wanda yake shiga irin ta turawa.
Misali; Ai yanzu ya zama gaye, kullum za ka gan shi da shigar nasara.
ENG; Cocky young person who wears western dress (A turance tana nufin gaye)