Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Generous - A turance tana nufin karimi.
Misali; Masha Allah ai Alhaji karimi ne ƙwarai da gaske.
HAU; Karimi (Tana nufin mutum mai girma da darajta mutane tare da kyautata musu)
Gentle person - A turance tana nufin kamili.
Misali; Malam Musa kamili ne.
HAU; Kamili (Tana nufin nagartaccen mutum mai kyawawan halaye)
Gero - Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai wanda ake amfani da shi wajen yin fura da kunu da sauransu.
Misali; Bana gero zalla ya shuka.
ENG; Millet (A turance tana nufin gero)
Gewaye - Tana nufi yi wa abu ƙawanya.
Misali; Ya gewaye gonarsa da kara saboda gudun dabbobi.
ENG; Surround (A turance tana nufin gewaye)
Ghost - A turance tana nufin fatalwa.
Misali; An ce fatalwar Idi tana fitowa da daddare.
HAU; Fatalwa (Tana nufin wanda ya mutu ya dinga gizo)
Giant Male Rat - A turance tana nufin burgu.
Misali; Da zan je makaranta na ga wani burgu ya shige rami da gudu.
HAU; Burgu (Tana nufin jibgegen namijin ɓera)
Giant Rat - A turance tana nufin gafiya.
Misali; Ramin gafiya ne a gurin.
HAU; Gafiya (Tana nufin ƙaton ɓera)
Gida - Tana nufin mazauni ko gini da ake yi don ba wa kai kariya daga abin cutarwa.
Misali; Ya gina ƙaton gida a sabuwar unguwa.
ENG: House (A turance tana nufin gida)
Gidan Rediyon Caina/Sin - China Radio International (CRI)
Gidan Rediyon Faransa - Radio France International (RFI)