Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Garaje - Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama.
Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan.
ENG; Quick Action/ Haste (A turance tana nufin garaje)
Garaya - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa na gargajiya.
Misali; Gurin ya cika da masu kiɗan garaya don bikin na 'yan bori ne.
ENG; Two stringed, plucked musical instrument (A turance tana nufin garaya)
Gare - Tana nufin rigar Hausawa mara ado.
Misali;Malam Audu ya sa gare.
ENG; Type of cloth without embroidery (A turance tana nufin gare)
Gargajiya - Tana nufin abubuwan da ake yi tun asali ko tun iyaye da kakanni.
Misali; Sarakunan gargajiya na da karamci.
ENG; Olden Times (A turance tana nufin gargajiya)
Kishiyarta; Zamani (Yanzu)
Gargaɗi - Tana nufin jan kunne ko yin hani.
Misali; Shugaban ɗalibai ya yi wa ɗalibai gargaɗi akan zuwa makaranta a makare.
ENG; Warning (A turance yana nufin gargaɗi)
Gari - Tana nufi inda mutane suka fi yawa musamman inda ba ƙauye ba (birni).
Misali; Abin mamaki, guri ya zama gari.
ENG; Town (A turance tana nufin Gari (Birni).
Kishiyarta; Ƙauye
Gari - Tana nufin niƙaƙken abu.
Misali; Mun siyo niƙaƙƙiyar masara za mu yi tuwo.
ENG; Flour (A turance tana nufin gari)
Garke - Tana nufin dabbobi da yawa, kamar akuyoyi, shanu da sauransu.
Misali; Yana da shanu garke guda.
ENG; Herd/Flock (A turance tana nufin garke)
Garma - Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai.
Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma.
ENG; Large hoe with wide blade (A turance tana nufin garma)
Garu - Tana nufin bango.
Misali; Ƙadangare yana yawo a juikin garu.
ENG; Wall (A turance tana nufin garu)