Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gamayyar Ƙungiyar ‘Ƴankasuwa Ta Afirka - Organization of Afirican Trade Union Unity (OATUU)
Gamayyar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Masana’antu da Kamfanonin Gwamnati da Wuraren Shaƙatawa Ta Ƙasa - Amalgamated Union of Public Corporations, Civil Service Technical & Recreational services Employees (AUPCTRE)
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa - Coalition of Northern Youth Groups (CNYG)
Gamayyar Ƙungiyoyin Sa-Kai - Civil Society Organizations (CSO)
Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago - United Labour Congress (ULC)
Gambling - A turance tana nufin caca.  Misali; A hanyar akwai dandalin da 'yan caca suke zama. HAU; Caca (Tana nufin wasan kati ne da ake sa kuɗi ko wani abu da zimmar wanda ya yi nasara ya ci wannan kuɗin ko abinda aka sa)
Game like draughts - A turance tana nufin dara. Misali; Da yamma ake wasan dara a majalisar. HAU; Dara (Tana nufin wasa da ake yi a kan katako mai faɗi, yana kama da wasan ludo)
Gammo - Tana nufin tsumman da ake nannaɗawa a sa a saman kai idan za a ɗauki kaya. Misali; Ka sa gammo a kanka saboda kayan na da nauyi. ENG; Head Pad (A turance tana  nufin gammo)
Gamsheƙa - Tana nufin ƙaton baƙin maciji. Misali; Mun ga gamsheƙa a hanyar gonar Malam Mudi. ENG: Black-hooded Cobra (A turance tana nufin gamsheƙa)
Ganawa - Tana  nufin tattaunawar sirri ko ta musamman. Misali; Shugaban makarantar na ganawa da malamai a ofishinsa. ENG; Private Discussion (A turance tana nufin ganawa)
1 109 110 111 112 113 300