Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gado - Tana nufin kuɗi da kadarorin da mamaci ke bar wa iyalansa, ma'ana duk abin da mutum ya mallaka idan ya mutu ya zama gado. Misali; Iyalan na rikici akan rabon gado. ENG; Inheritance (A turance tana nufin gado)
Gafaka - Tana nufin jakar fata da ake yi musamman don saka littattafai. Misali; Malamin ya saka Al'ƙur'ani a gafaka. ENG; Satchel (A turance tana nufin gafaka)
Gafara - Tana nufin yafiya musamman ta Allah SWT. Misali; Allah mai gafara ne ga bayinsa. ENG; Pardon/Forgiveness (A turance tana nufin gafara)
Gafiya - Tana nufin ƙaton ɓera. Misali; Ramin gafiya ne a gurin. ENG; Giant Rat (A turance tana nufin gafiya)
Gagarumi - Tana nufin babban abu mai muhimmanci. Misali; Gwamnati ta haɗa gagarumin taron masu sana'o'in gargajiya. ENG; Big/Important (A turance tana nufin gagarumi)
Gaggauta - Tana nufin a yi abu da sauri ko hanzari. Misali; Ku gaggauta gamawa saboda lokacin tashi ya yi. ENG; Hurry (A turance tana nufin gaggauta)
Gajere - Tana nufin mara tsayi. Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar. ENG: Short (A turance tana nufin gajere)
Gajiya - Tana nufin mutuwar jiki da jin rashin ƙarfi. Misali; Gudu na sa gajiya sosai. ENG; Tiredness (A turance tana nufin gajiya)
Galadima - Tana nufin muƙamin sarauta. Misali; An naɗa malam Sani galadima jiya da safe. ENG; A traditional title (A turance tana nufin galadima)
Galibi - Tana nufin mafi yawa. Misali; Galibi akan yi ruwa mai yawa a watan Agusta. ENG; Majority (A turance tana nufin galibi)
1 108 109 110 111 112 300