Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fried cake made of wheat flour - A turance tana nufin fanke.
Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar.
HAU; Fanke (Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu)
Frog - A turance tana nufin kwaɗo.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
HAU; Kwaɗo (Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa)
Fronds of Dum-palm - A turance tana nufin kaba.
Misali; Tabarmar da muke zaune ta kaba ce.
HAU; Kaba (Tana nufin ganyen bishiyar goruba da ake amafani da shi wajen yin tabarma da mafici da sauransu)
Fruitless Search - A turance tana nufin bilimbituwa.
Misali; Mafarautan bilimbituwa kawai za su yi a dajin saboda babu namun daji yanzu.
HAU; Bilimbituwa (Tana nufin neman abu a rasa a yi ta bulayi, ko kuma neman da babu sakamako)
Fulfilment Of Wish - A turance tana nufin ijaba.
Misali; Allah ya yi mana ijaba, yau ruwa ya sauka.
HAU; Ijaba (Tana nufin cikar buri)
Full stop - A turance tana nufin aya.
Misali; Aya alama ce da ke nuna jimla ta zo ƙarshe.
HAU; Aya (Alama ce ta dakatawa a cikin rubutu)
Fund - Asusu, Gidauniya
Funeral - A turance tana nufin jana'iza.
Misali; Za a yi jana'iza a babban masallacin Juma'a yau.
HAU; Jana'iza (Tana nufin sallar da ake yi wa mamaci kafin a kai shi kabari)
Fura - Tana nufin abin sha da ake yi da gero.
Misali; An dama mana fura da nono.
ENG; Balls made of cooked millet (A turance tana nufin fura)
Fure - Tana nufin tsiro mai ban sha'awa mai ɗauke da launi daban-daban.
Misali; An tsinko fure daga lambu.
ENG; Flower (A turance tana nufin fure)