Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fatauci - Tana nufin tafiya daga wani gari zuwa wani gari don siye da siyar da kaya.
Misali; Idi ya tafi fatauci wata biyu da suka wuce.
ENG; Trading (A turance tana nufin fatauci)
Father - A turance tana nufin mahaifi.
Misali; Baba yana da jikoki arba'in a yanzu.
HAU; Baba (Tana nufin mahaifi)
Fatness - A turance tana nufin ƙiba.
Misali: Ƙiba mai yawa na iya jawo matsaloli ga lafiya.
HAU: Ƙiba (Tana nufin girma ko nauyin jiki)
Fatsa - Tana nufin abin kama kifi.
Misali; Ya ɗauki fatsa ya nufi kogi zai yi su.
ENG; Fish-hook (A turance tana nufin fatsa)
Fawa - Tana nufin sana'ar siyar da nama.
Misali; Wanda zai aure ta fawa yake.
ENG; Butchering (A turance tana nufin fawa)
Fayyace - Tana nufin yin cikakken bayani.
Misali; Malamin ya fayyace mana darasin dalla-dalla.
ENG; Explain Thoroughly (A turance tana nufin fayyace)
Faɗa - Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai.
Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta.
ENG; Quarrel (A turance tana nufin faɗa)
Faƙiri - Tana nufin talaka wanda ba shi da komai.
Misali; Idan za ka yi sadaka ka nemi faƙiri ka ba shi.
ENG; Poor, Destitute (A turance tana nufin faƙiri)
February - A turance yana nufin wata na biyu a shekara.
Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar.
HAU; Fabrairu (Wata ne na biyu a shekara)
Feda - Tana nufin inda ake sa ƙafa a tuƙa keke.
Misali; Keken na da matsalar feda sai an gyara.
ENG; Bicycle Pedal (A turance tana nufin feda)