Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Feƙe - Tana nufin saka abu ya yi kaifi. Misali; An feƙe wuƙaƙen kafin a yanka naman. ENG; Sharpen (A turance tana nufin feƙe)
Fifth month of Islamic calendar - A turance tana nufin jimada awwal. Misali; A watan Jimada Awwal za a yaye ɗaliban. ENG; Jimada Awwal (Tana nufin wata na biyar a watannin musulunci)
Fifty - A turance tana nufin hamsin. Misali; Bulalar da aka yi masa ta kai hamsin. HAU; Hamsin (Tana nufin goma sau biyar)
Fige - Tana nufin cire gashi. Misali; Na biya kuɗi an fige min kajin da na siya. ENG; Pluck (hair, feathers)(A turance tana nufin fige)
Filla-filla - Tana nufin daki-daki. Misali; Ya yi mana bayani filla-filla. ENG; Step by step (A turance tana nufin filla-filla)
Financial Market Dealers Association (FMDA) - Ƙungiyar Dillalan Hada-hadar Kuɗi Ta Najeriya
Financil Reporting Council of Nigeria (FRCN) - Hukumar Rawaito Hada-hadar Kuɗi Ta Najeriya
Fincika - Tana nufin jan abu da ƙarfi. Misali; Ta tsinka jakar da ta fincika. ENG; Pull out suddenly with force (A turance tana nufin fincika)
Find Fault - A turance tana nufin kushe. Misali; Duk yanda abu ya kai da kyau mahassada sai sun kushe shi. HAU; Kushe (Tana nufin faɗar aibu ko ƙaƙalo laifin abu)
Fingernail - A turance tana nufin farce. Misali; Salihu yana sana'ar yankan farce. HAU; Farce (Tana nufin ƙumba)
1 102 103 104 105 106 300