Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Federation - Kadaura, Ƙungiya, Tarayya
Federation Account Allocation Committee (FAAC) - Kwamitin Kasafta Lalitar Gwamnatin Tarayya
Federation of Construction industry (FOCI) - Kadaurar Masana'antun Kwangila
Federation of International Football Association (FIFA) - Hukumar Ƙwallon Kafa Ta Duniya
Federation of Tourism Associations of Nigeria (FTAN) - Kadaurar Ƙungiyoyin Yawon Buɗe-Ido Ta Najeriya
Feed Animal - A turance tana nufin kiwata.
Misali; Zan kiwata Saniyar da aka ba ni har ta hayayyafa.
HAU; Kiwata (Tana nufin ciyarwa ta tsahon lokaci )
Female Slave - A turance tana nufin kuyanga.
Misali; Mallakar kuyanga sai masu hannu da shuni.
HAU; Kuyanga (Tana nufin baiwa mace)
Fensir - Tana nufin abin rubutu.
Misali; 'Yan aji ɗaya da fensir suke rubutu.
ENG; Pencil (A turance tana nufin fensir)
Fetur - Tana nufin man da ake zubawa a mota ko wani abin hawa don ya yi tafiya.
Misali; Fetur ya yi matuƙar tsada a Najeriya.
ENG; Petrol (A turance tana nufin fetur)
Few - A trurance tana nufin kaɗan.
Misali; Sun yi aiki mai yawa amma ya ba su kuɗi kaɗan.
HAU; Kaɗan (Tana nufin babu yawa)`
Kishiyarta; Da yawa