Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fool - A turance tana nufin dolo. Misali; Yaron dolo ne, ya samu matsalar ne tun daga haihuwa. HAU; Dolo (Tana nufin wanda yake da ƙarancin hankali da fahimta)
Football Writers Association (FWA) - Ƙungiyar Marubuta Wasan Ƙwallon Ƙafa
Fore-arm - A turance tana nufin damtse. Misali; Masu manyan damtse yawancin su ƙarfafa ne. HAU; Damtse (Tana nufin gaɓar da take saman hannu)
Forehead - A turance tana nufin goshi. Misali; Ya fasa goshi garin wasan banza. HAU; Goshi (Tana nufin gaɓar da ke saman gira)
Forestry Research Institute of Nigeria (FRIN) - Cibiyar Nazarin Gandun Daji Ta Najeriya
Forum - Ƙungiya, Kadaura
Foundation - A turance tana nufin harsashi. Misali; An dasa harsashin gina makarantar islamiyya a yankin mu. HAU; Harsashi (Tana nufin tushe)
Foundation - Gidauniya
Four - A turance tana nufin huɗu. Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu. HAU; Huɗu (Tana nufin lambar da ke bin bayan uku)
Friday - A turance tana nufin rana ta biyar a mako.  Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a. HAU; Juma'a (Rana ce ta biyar a ranakun mako)
1 105 106 107 108 109 300