Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Furfura - Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa.
Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina.
ENG; Grey Hair (A turance tana nufin furfura)
Furuci - Tana nufin yin magana.
Misali; Yana da furuci daddaɗa.
ENG; Utterance (A turance tana nufin furuci)
Fusata - Tana nufin tsananin fushi.
Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake.
ENG; So Angry (A turance tana nufin fusata)
Fuska - Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki.
Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa.
ENG; Face (A turance tana nufin fuska)
Fyace - Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi.
Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai.
ENG; Blow One's Nose (A turance tana nufin fyace)
Fyaɗa - Tana nufin duka musamman da tsumagiya.
Misali; Ai alamajirin nan ya sha fyaɗa a gurin malaminsu.
ENG; Whip, Flog (A turance tana nufin fyaɗa)
Fyaɗe - Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba.
Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya.
ENG; Rape (A turance tana nufin fyaɗe)
Gaba - Tana nufin daina yi wa juna magana.
Misali; Ai sun daɗe suna gaba da juna saboda dalilin da bai kai ya kawo ba.
ENG; Enmity (A turance tana nufin gaba)
Gabani - Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki.
Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta.
ENG; The time just before (A turance tana nufin gabani)
Gado - Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta.
Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa.
ENG; Bed (A turance tana nufin gado)