Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gane - Tana nufin fahimta.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
ENG; Understand (A turance tana nufin gane)
Kishiyarta; Rashin Ganewa
Ganganci - Tana nufin yin abu ba tare da kula ba ko gaba-gaɗi.
Misali; Tuƙin gangancin da direban yake yi ne ya janyo hatsarin.
ENG; Acting in a careless way (A turance tana nufin ganganci)
Ganima - Tana nufin kayayyakin da ake samu bayan kammala yaƙi, kamar bayi, kuɗi da sauransu.
Misali; An samu ganima mai yawa a yaƙin.
ENG; Booty (A turance tana nufin ganima)
Gansakuka - Tana nufin wani koren abu da yake fitowa a guraren da danshi yake.
Misali; Bangon duk ya yi gansakuka saboda damina.
ENG;Green slime collecting on stagnant water (A turance tana nufin gansakuka)
Gantali - Tana nufin tsananin yawo.
Misali; Mijin ya saki matar ne saboda tana da gantali.
ENG; Aimless Wandering (A turance tana nufin gantali)
Ganuwa - Tana nufin ginin da ake yi don katange gari da ba shi kariya.
Misali; An ɗauki shekaru ana gina ganuwar Jihar Kano.
ENG; Town Wall (A turance tana nufin ganuwa)
Ganɗa - Tana nufin saman bakin mutum.
Misali; Ƙuraje sunm fito masa a saman ganɗa, sun hana shi cin abinci.
ENG; Roof Of The Mouth (A turance tana nufin ganɗa)
Gap from loss of tooth - A turance tana nufin giɓi.
Misali; Ta samu giɓi sakamakon haƙorinta ɗaya da ya fita.
HAU; Giɓi (Tana nufin gurbin mai faɗi da ke tsakanin haƙora)
Gara - Tana nufin ƙwaron da yake cinye katako.
Misali; Gara ta cinye kujerun duk sun lalace.
ENG; Termites (A turance tana nufin gara)
Gara - Tana nufin kayan masarufi da iyayen mace ke haɗota da su bayan aure.
Misali; An yi wa amaryar gara ta ban mamaki.
ENG; Presents of foodstuffs given by parents of bride to parent of groom (A turance tana nufin gara)