Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Garwashi - Tana nufin diddigar wuta.
Misali; Ta yi amfani da garwashi wajen gasa cibiyar jaririn.
ENG; Hot Embers (A turance tana nufin garwashi)
Garɗi - Tana nufin wani nau'in ɗanɗano mai daɗi a baki.
Misali; Madarar tana da garɗi sosai.
ENG; Nutty Flavour (A turance tana nufin garɗi)
Gas Exporting Countries Forum (GECF) - Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Iskar Gas
Gasa - Tana nufin gwaji ko auna tsakanin abubuwa guda biyu don fitar da wanda ya fi.
Misali; An sa gasa tsakanin 'yan aji biyu da 'yan aji uku.
ENG; Competition (A turance tana nufin gasa)
Gashi - Tana nufin tsiron da ke fitowa a saman fatar ɗan Adam ko dabba.
Misali; Mata sun fi maza yawan gashi.
ENG; Hair (A turance tana nufin gashi)
Gaskata - Tana nufin yarda.
Misali; Mun gaskata annabinmu SAW.
ENG; Believe (A turance tana nufin gaskata)
Kishiyarta; Ƙaryata
Gaskiya - Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi.
Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa.
ENG; Truth (A turance tana nufin gaskiya)
Kishiyarta; Ƙarya
Gasping noises made by animal whose throat has been cut - A turance tana nufin kakari.
Misali; an daɗe da yanka saniyar amma har yanzu tana ta kakari.
HAU; Kakari (Tana nufin ƙarar da ke fitowa sakamakon toshewa ko yanka maƙogwaro, musamman idan an yanka dabba)
Gata - Tana nufin samun duk abinda ake buƙata na rayuwa.
Misali; 'Ya'yan Alhaji Jibrin na da gata saboda ya sa su a makaranta mai tsada.
ENG: Caring For (A turance tana nufin gata)
Gatari - Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen saran itace.
Misali; Icen ba zai fasu ba sai an sa gatari.
ENG; Axe (A turance tana nufin gatari)