Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Giɓi - Tana nufin gurbin mai faɗi da ke tsakanin haƙora.
Misali; Ta samu giɓi sakamakon haƙorinta ɗaya da ya fita.
ENG; Gap from loss of tooth (A turance tana nufin giɓi)
Gladden - A turance tana nufin faranta.
Misali; Matar ta faranta ran mijinta ta hanyar yi masa girki.
HAU; Faranta (Tana nufin sanya farin ciki)
Glare At - A trurance tana nufin harara.
Misali; Harara ta yake don na dake shi.
HAU; Harara (Tana nufin kallon raini ko wulaƙanci)
Goat or sheep skin used as prayer mat - A turance tana nufin buzu
Misali; Malam yana sallah akan buzu a lokacin da na je.
HAU; Buzu (Tana nufin abin da ake salla a kai wanda aka yi shi da fatar akuya ko tinkiya)
Goat Skin Bag - A turance tana nufin burgami.
Misali; Malam Yahaya ya ratayo burgami a gurin bikin maharba.
HAU; Burgami (Tana nufin jakar da aka yi ta fatar akuya, wadda yawanci masu ba da maganin gargajiya ke amfani da ita)
Goats - A turance tana nufin jam'in akuya.
Misali; Kaka yana kiwon awaki.
HAU; Awaki (Jam'in akuya)
Goba - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari tana da ƙananan ƙwallaye a cikinta.
Misali; Goba tana da sinadarai masu inganta lafiya a cikinta.
ENG; Guava (A turance tana nufin goba)
Gobe - Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki.
Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako.
ENG; Tomorrow (A turance tana nufin gobe)
Kishiyarta; Yau
God - A turance tana nufin jalla.
Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau.
HAU; Jalla (Tana nufin Allah maɗaukakin sarki)
Godiya - Tana nufin yabawa.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
ENG: Thanks (A turance tana nufin godiya)
Kishiyarta; Rashin Godiya