Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gogagge - Tana nufin ƙwarewa a wani abu ko wani fanni.
Misali; Ai malamin gogagge ne a fannin kimiyya da fasaha.
ENG; Skilled (A turance tana nufin gogagge)
Going back and forth - A turance tana nufin jigila.
Misali; Kamfanonin jiragen sama na ta jigilar alhazai daga ƙasashe daban-daban.
HAU; Jigila (Tana nufin kai wa da komowa (kai-komo))
Going to and fro - A turance tana nufin jewa.
Misali; Na gan shi yana ta jewa saboda tashin hankali.
HAU; Jewa (Tana nufin je-ka-ka-dawo)
Goma - Tana nufin lambar da ke bin bayan tara.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
ENG; Ten (A turance tana nufin goma)
Gomiya - Tana nufin goma sau wani adadi.
Misali; Gomiya biyar tana nufin hamsin kenan.
ENG; Multiple Of Ten (A turance tana nufin gomiya)
Gona - Tana nufin fili ko sararin da ake shuka a yi noma.
Misali; Yana da gona amma ya gaje ta ne a gurin mahaifinsa.
ENG; Farm (A turance tana nufin gona)
Gona - Gona wuri ne da ake shuka abinci da kuma kayan marmari ( kayan lambu) kamar su tumatur,kabeji,alayyahu,shinkafa,masara,dawa,gero da dai sauransu.
Good News - A turance tana nufin bishara.
Misali; Malamin ya yi wa ɗalibai bishara da cinye jarabawarsu.
HAU; Bishara (Tana nufi labari mai daɗi)
Goods/Loads - A turance tana nufin kaya.
Misali; Motar ɗaukan kaya yake ja yanzu.
HAU; Kaya (Tana nufin abubuwa da yawa)
Goro - Tana nufin ɗan itaciya da ake ci mai ƙunshe da muhimman abubuwa masu inganci.
Misali; An raba goro a gurin ɗaurin auren.
ENG; Kolanut (A turance tana nufin goro)