Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Grave - A turance tana nufin kushewa.
Misali; An kai ta kushewa tun safe da aka yi jana'izarta.
HAU; Kushewa (Tana nufin kabari)
Grave - A turance tana nufin kabari.
Misali; Ya daɗe yana sana'ar haƙar kabari.
HAU; Kabari (Tana nufin ramin da ake binne mamaci)
Greed - A turance tana nufin haɗama.
Misali; Saboda haɗama ya kwashe abincin mutum uku shi kaɗai.
HAU; Haɗama (Tana nufi wawashe abu da yawa musamman idan ana haɗawa da rabon wasu)
Green - A turance tana nufin kore.
Misali; Kayan makarantarsu kore ne.
HAU; Kore (Tana nufin launi)
Green slime collecting on stagnant water - A turance tana nufin gansakuka.
Misali; Bangon duk ya yi gansakuka saboda damina.
HAU; Gansakuka(Tana nufin wani koren abu da yake fitowa a guraren da danshi yake)
Greeting - A turance tana nufin barka.
Misali; Ina yi muku barka da yamma.
HAU; Barka (Tana nufin gaisuwa)
Grey Hair - A turance tana nufin furfura.
Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina.
HAU; Furfura (Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa)
Grind Coarsely - A turance tana nufin ɓarza.
Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma.
HAU; Ɓarza (Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba)
Ground Squirrel - A turance tana nufin kurege.
Misali; Ado ya bi kurege har cikin raminsa ya kamo shi.
HAU; Kurege (Tana nufin wata dabba mai kama da zomo)
Groundnut - A turance tana nufin gyaɗa.
Misali; Ina son dafaffiyar gyaɗa.
HAU; Gyaɗa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abin ci mai ɗauke da sinadaren gina jiki, ana sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban)