Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Growling - A turance tana nufin gurnani. Misali; Ba zan iya shiga gidan ba, na jiyo kare yana gurnani. HAU; Gurnani (Tana nufin gunji da dabbobi ke yi musamman kare da zaki)
Gruel made of guinea-corn or millet flour - A turance tana nufin kunu. Misali; An dama wa mai jego kunu. HAU; Kunu (Tana nufin abin sha wanda ake yi da gari ko markaɗaɗɗen gero mai ƙunshe da kayan ƙamshi da tsamiya ko kanwa)
Guava - A turance tana nufin goba. Misali; Goba tana da sinadarai masu inganta lafiya a cikinta. HAU; Goba (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari tana da ƙananan ƙwallaye a cikinta)
Guba - Tana nufin duk wani abin da zai iya kisa. Misali; Na sa wa ɓeraye guba jiya da yamma. ENG; Poison (A turance tana nufin guba)
Guda - Tana nufin ɗaya. Misali; Gida guda za mu zauna da ƙani na. ENG; One (A turance tana nufin guda)
Gudanar - Tana nufin aiwatarwa. Misali; An gudanar da taron a gidan adana ababen tarihi. ENG; Administer (A turance tana nufin gudanar)
Gudanarwa - Yadda ake tafiyar da aiki ko wani al'amari bisa wani tsari da dokoki na musamman.
Gudawa - Tana nufin yin bayan gida (kashi) akai-akai kuma mai ruwa-ruwa, a wasu lokutan ma har da ciwon ciki. Misali; Tun jiya yake gudawa amma ya sha magani yanzu. ENG; Diarrhoea (A turance tana nufin gudawa)
Gudu - Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri. Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri. ENG; Run (A turance tana nufin gudu)
Guduma - Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen buga katako ko ƙusa da sauransu. Misali; Ya buge hannu da guduma a lokacin da yake gyaran kujerar. ENG; Hammer (A turance tana nufin guduma)
1 122 123 124 125 126 300