Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gumi - Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu. Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake. ENG; Sweat (A turance tana nufin gumi)
Gun - A turance tana nufin bindiga. Misali; Sojoji sun kama wani matafiyi da bindiga a hanyar Sokoto. HAU; Bindiga (Tana nufin na'aurar harbi musamman ga mayaƙa ko maharba ko jami'an tsaro)
Gunaguni - Tana nufin yin ƙorafi ko magana ƙasa-ƙasa ba tare wanda ake yi don shi ya fahimci abinda ake faɗa ba. Misali; Habu yana ta gunaguni saboda Shamsu ya dake shi. ENG; Complaining (A turance tana nufin gunaguni)  
Gunduma - Tana nufin ɗibgawa ko yi wa mutum gagarumin laifi. Misali; An gunduma wa 'yan kasuwar sata. ENG; Do much of evil act (A turance tana nufin gunduma)
Gundura - Tana nufin jin abu ya fita daga rai. Misali; Kallon wasan ƙwallon ƙafa ya gundure ni. ENG; Lose Interest (A turance tana nufin gundura)
Gunki - Tana nufin sassaƙaƙƙen abu musamman wanda ake bautawa, zai iya kasancewa mai siffar mutum ko dabba da sauransu. Misali; Indiyawa na da gunki a gidajensu, don sun yarda shi ne abin bautarsu. ENG; Idol (A turance tana nufin gunki)
Guntu - Tana nufin mara tsayi. Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin. ENG; Short (A turance tana nufin guntu) Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Guntule - Tana nufin yanke wani sashi. Misali; A musulunci hukuncin sata shi ne guntule hannu. ENG; Cut Short (A turance tana nufin guntule)
Gurasa - Tana nufin nau'in abinci da ake yi da fulawa kuma gasa ta ake yi a tanderu. Misali; Na yi banɗashen gurasa a matsayin abincin rana. ENG; Baked-wheat cake (A turance tana nufin gurasa)
Gurfana - Tana nufin durƙusawa a kan gwuiwa biyu. Misali; Masu laifin sun gurfana a gaban alƙali. ENG; Kneel with front elbows on ground (A turance tana nufin gurfana)
1 124 125 126 127 128 300