Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gudunmawa - Tana nufin tallafi ko agaji. Misali; Gwamnati ta kawo gudunmawa ga waɗanda ibtila'in gobara ya afkawa. ENG; Help (A turance tana nufin gudunmawa)
Guguwa - Tana nufin iska mai ƙarfi. Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa. ENG; Whirlwind (A turance tana nufin guguwa)
Guild - Kadaura, Ƙungiya, Majalisa
Guinea Corn - A turance tana nufin dawa. Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya. HAU: Dawa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi)
Guinea-worm - A turance tana nufin kurkunu. Misali; An yi nasarar kawar da cutar kurkunu a Najeriya. HAU; Kurkunu (Tana nufin cutar fata mai sanya ƙuraje)
Gujjiya - Tana nufin nau'in abin ci mai kama da wake amma ta fi wake girma, kuma a cikin kwanso take, sai an ɓare. Misali; Ina son gujjiya sosai, na ji an ce har tuwonta ake yi. ENG; Bambara Groundnut (A turance tana nufin gujjiya)
Gulbi - Tana nufin kwari da ruwa yake taruwa. Misali; Indo da ƙawayenta sun tafi gulbi yin wanki. ENG; River (A turance tana nufin gulbi)
Gulma - Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa. Misali; Musulunci ya haramta gulma. ENG; Setting one person against another through gossip (A turance tana nufin gulma)
Gum - A turance tana nufin danƙo. Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa. HAU; Danƙo (Tana nufin abu mai mannewa)
Gumba - Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa. Misali; An raba gumba a gidan mutuwar. ENG; Sweet pounded millet mixed with water (A turance tana nufin gumba)
1 123 124 125 126 127 300