Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Fish Cake

    Yadda Ake Fish Cake

    Fish cake wani abu ne wanda ake haɗa shi da kifi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Farin kifi 8 (dafaffe)
    • Dankali 8 (dafaffe)
    • Cokali 1 na kayan ƙamshi
    • Cokali 1 na ruwan lemon tsami
    • Kwai guda 1
    • Butter cokali 1
    • Tafarnuwa 1
    • Abin ɗanɗano/attaruhu da albasa

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Abin daka
    • Kasko
    • Kwano/paranti
    • Cokali

    Yadda Za A Haɗa Fish Cake

    A ɗan daka ɗankali sama–sama, sannan a zare ƙayar kifin, a daka tafarnuwa da kayan ƙamshi a haɗa da sauran gaba ɗaya da attaruhu da albasa duk a haɗa, a cakuɗa su gaba ɗaya.

    Sai a dunƙula gaba ɗaya, daga nan sai a ɗan danno shi ya koma kamar ƙosai a ɗan barbaɗa fulawa a tsoma a ruwan kwai sannan a soya mai me zafi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake CupCake danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Potato Cake. ko Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Miyar Kayan Ciki

    Yadda Ake Miyar Kayan Ciki

    Miyar kayan ciki wadda aka fi sani da pepper soup; Wannan miya ana haɗa ta ne da kayan ciki kamar su hanji, hanta da dai sauransu.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Miyar su ne:

    • Tumbi
    • Kitse
    • Hanta
    • Zuciya – huɗu
    • Albasa
    • Salt & maggi (abin ɗanɗano da gishiri)
    • Markaɗe
    • Tafarnuwa
    • Masoro
    • Girfa
    • Habbahan

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Tukunya
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Cokali
    • Abin daka
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami tumbi da kitse da hanta da zuciya da huhu da kuma hanji, sai a sami ruwa a tafasa a ɗauko hanjin, sai a samu mutum biyu, ɗaya ya riƙe ɗayan gefen.

    Sai a tsoma shi cikin ruwan zafi sai a sa wuƙa a kankare shi, sai ya yi haske, sai a yayyanka ƙanana, sai a wanke hanjin sosai a tabbatar ya wanku a tsane

    Sannan a sa albasa da mai da gishiri da kuma maggi, za a ga ya yi ruwa, sai a sa markaɗe irin na farko, in ruwan ya yi kaɗan a ɗan ƙara a bar shi ya yi ɗan kauri 

    Daga ƙarshe, a ɗauko tafarnuwa a daka da masoro a jefa girfa a ciki da habbahan a juya in ta yi a sauke

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Miyar Agushi danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Miyar Gyaɗa. danna nan

  • Yadda Ake Kufta

    Yadda Ake Kufta

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Kufta su ne:

    • Niƙaƙƙen nama
    • Abin ɗanɗano
    • Tafarnuwa
    • Shammar
    • Masoro 
    • Gishiri

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Cokali
    • Abin daka

    Yadda Ake Haɗawa

    Za a niƙa nama dai-dai yadda ake buƙata, sai a sa masa abin ɗanɗano daidai yadda yai miki, ki sa shamma da tafarnuwa da kuma masoro, sai a zuba gishiri kaɗan, sai a haɗa da mai kaɗan, a cakuɗa, ya haɗa jikinsa.

    Sai a riƙa cirar naman ana cuccurawa ko duddunƙulawa, dogo–dogo, sai a soya a mai me zafi.

    Miyar da Ake Ci Da Kufta

    Za a iya yi masa miya a ci da ita, a samu markaɗe na tumatur mai yawa, tattasai kaɗan, sai ki zuba a tukunya, ki sa masa ‘yar kanwa, ki sa mai, a sa masa tafarnuwa (dakakkiya), a sa abin ɗanɗano a bar ta ta yi kauri kamar faten doya, sai a sa naman a ciki ya yi minti 1 ko 2, sai a sauke za a iya ci da dogon biredi ko shinkafa ko taliya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gima Macaroni Jallof danna nan

  • Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP)

    Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP)

    Kebab wani abinci ne da ake haɗa shi da nama, tare tumatir da dai sauransu.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Kebab su ne:

    • Kidney, liver, meat (ƙoda, hanta, nama)
    • Onions (albasa)
    • Markaɗe
    • Spices (kayan ƙamshi )
    • Salt, maggi (gishiri da abin ɗanɗano)
    • Mai

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kwano
    • Cokali
    • Wuƙa
    • Kasko

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami ƙoda da hanta da nama (na rago) duk sai ki tafasa, ki yanka su triangle ƙanana, sai ki sami albasa ki soya, ki kawo mai kaɗan ki zuba.

    In yasoyu ki zuba mai, kibar ta tayi kauri sai ki saka dan kalin da naman acikin miyar.

    Sannan ki sa kayan ƙamshi, idan ya haɗu a sauke.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Fish Soup danna nan

  • Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa

    Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa

    Yaushe mata suka fara jinin haila?

    Farkon fara jinin haila ya kasance ne a kan Hauwa’u matar Annabi Adamu, amincin Allah ya tabbata a gare su;

    Bayan an sauko da su daga Aljanna zuwa duniya. Sannan Allah ya hukunta shi a kan ‘ya’yan Annabi Adamu mata.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa ya ce, “Haƙiƙa, wannan wani al’amari ne da Allah ya hukunta shi a kan ‘ya’yan Annabi Adamu mata” .

    Mece ce sifar jinin Haila?

    Jinin haila baƙi ne, mai wari, kuma ƙazanta ce. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya ce, “Haƙiƙa, shi jinin baƙi ne kuma yana da ƙarni, kuma Allah tsarkakakke maɗaukaki ya ce:

    “Kuma suna tambayar ka game da jinin haila, ka ce da su ƙazanta ne…”. Kuma shi wannan jinin yakan zo ja ko fatsi-fatsi, mai baƙi kuma a ƙarshensa, yakan canja ruwan ƙasa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ambaton Abin Da Ake Sanin Zuwan Jinin Al’ada Da Shi Da Yankewar sa danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ki Gyara Kanki danna nan.

  • Jinin Haila Da Jinin Biƙi

    Jinin Haila Da Jinin Biƙi

    Darasi Na Farko Game Da Jinin Da Yake Fita Daga Mace

    Game Da Jinin Da Yake Fita Daga Mace, Jini Nawa Ne Yake Fita Daga Mace? 

    Jini Uku Ne Yake Fita Daga Mace, su ne: Jinin Haila, Jinin Biki da Jinin Cuta.

    Mece ce Haila?

    Haila ita ce jinin da yake fita daga mahaifar mace idan ta balaga, a wasu kwanaki sanannu. 

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa ya ce da Hannatu ‘yar Jahshi.

    Ki yi hailarki kwana shida, ko kwana bakwai. Hakan sai ya zama shi ne galibin kwanakin jinin haila, kuma yana iya ƙasa da haka ko ya ƙaru.

    Mene ne Jinin Biƙi?

    Jinin biƙi shi ne jinin da yake fita daga gaban mace saboda haihuwa ko da abin da aka Haifa ɓari ne.

    Mene ne Jinin cuta?

    Jinin cuta shi ne, ci gaban fitar jini daga gaban mace saboda rashin lafiya, ba a lokacin jinin haila. kuma ba a lokacin jinin biƙi ba.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya? danna koren rubutun nan.

  • Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta?

    Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta?

    Mutane da dama suna amfani da Komfiyuta wurin samun sauƙin aikinsu na yau da kullum. Misali idan muka duba; mutum zai iya ɗauko aiki daga ofishinsa zuwa gida domin ƙarasa aikin da ya fara a can.

    Haka ɗalibai suna iya ci gaba da nazari ko binciken da suka fara a Komfiyutar makaranta idan sun dawo gida, wannan aiki kuwa mutum zai iya yin amfani da safe ko da rana ko cikin dare;

    Haka mutum zai iya amfani da wannan kwamfutar domin tafiyar da harkokin kasuwancinsa ta hanyar rubuta wasiƙa; ko waɗansu bayanai masu muhimmanci na kasuwancinsa, ko kuma shirya kasafin kuɗi.

    A taƙaice dai duk wani irin aiki da za ka iya yi da Komfiyutar wurin aiki; za ka iya yin shi da kwamfutar da ita a cikin gida.

    Lura Da Hada-Hadar Kuɗaɗe Da Kasuwanci

    Ba ka buƙatar zama ƙwararren masanin harkokin kuɗi wurin kula da kuɗaɗenka da kasuwancinka idan aka zo maganar Komfiyuta.

    Akwai waɗansu manhajoji a cikin Komfiyuta waɗanda da su za ka iya lura da kuɗaɗe kamar irin su Microsoft money ko kuma Quicken wanda da waɗannan za ka iya shirya kasafin kuɗi.

    Ko kuma rubuta takardun karɓar kuɗi ko kuma bincikar labarin ragowar kuɗaɗen da suke asusunka; da ke bankinka take daga jikin kwamfutarka ba tare da kana da ilmin a kanta ba.

    Haka zalika, za ka iya sanya kwamfutarka ta ɗauki ragamar biyan kuɗaɗe ta banki da kanta na haƙƙoƙin jama’a ko biyan kuɗaɗen harajin gwamnati, wanda ba sai ka je banki don gabatarwa ba.

    Ƙulla Alaka Tsakanin Mutane

    Da kwafuta ana iya aikawa da wasiƙa wacce ake kira da imel [email] ga ‘yan uwa da abokan arziƙi ba ka buƙatar jiran lokaci mai tsawo kafin wannan saƙo ya kai ga wurin daka aika shi.

    Haka ana amfani da kwamfuta wurin yin magana ko muhawara da jama’a kai tsaye ta hanyar amfani da intanet.

    Ko kuma kiran kwamfuta da wata kwamfuta wanda aka fi sani da pc to pc call; wannan duk wani sauƙi ne ake samu a wurin kwamfuta.

    Yin Hada-Hada A Intanet

    Kamar yadda muka faɗi, amfani da fasahar email ya kawo sauƙi wurin aikawa da saƙonni haka ma intanet.

    Internet wata kafa ce da mutane ke amfani da ita wurin gabatar da abubuwa masu muhimmanci da kuma aikace-aikacen da suka saba yi a zahiri da jama’ a.

    Kamar gabatar da harkokin kasuwanci wanda ya haɗa da sayarwa, yin karatu da manyan jami’o’i na duniya, karanta jaridu da mujallu duk a kan intanet, alhali mutum na zaune a gida ko ofishinsa waɗannan kaɗan ne daga cikin irin aikace-aikacen da ita komfiyuta take iya yi da kuma sauƙin gabatar da al’amura.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan

  • Yadda Ake Activating Windows 10 Da Batch File (CMD)

    Yadda Ake Activating Windows 10 Da Batch File (CMD)

    Idan ka yi amfani da wannan hanya ba tare da ɓata lokaci ba za ka ba wa windows 10 ɗinka damar yin aiki sosai.

    Kuma hakan bai da wata matsala. Na kawo wannan ne saboda yin amfani da wata manhaja ka iya janyo matsala.

    Misali kamar yin amfani da KMSpico a wasu lokutan.

    Za ka iya buɗe Notepad a kan kwamfutarka mai ɗauke da Windows 10 wadda take buƙatar a yi activating ɗin ta.

    Ga waɗansu matakai da za a bi domin aiwatarwa:

    1. Ka juyi wannan, ka mayar da shi a kan tsarin text file.

    2. Sai ka ajiye shi wannan abun da ka juya a matsayin batch file ɗin, sai kuma ka canja masa suna zuwa (Smartrogo.cmd)

    3. Sai a danna madannin dama na kan mouse a kan shi file ɗin da aka ajiye, sai a danna madannin hagu a kan ‘Run as administrator’.

    4. Sai a duba a gani, domin sanin matsayin activating ɗin da aka yi .

    Da zarar ka danna kan “Run as administrator” zai ɗan nuna maka cewar ya shiga kan system command prompt – kar ka damu yana kan aiki ne.

    da zarar ya kamala gabatarwa, sai ka danna alamar “Y “. Wanda hakan shi zai ba ka damar kashe kwamfutarka, ya kuma kunna ta, sai ka ga Activating ɗin ya yi.

    Za kuma ka iya duba cewar “Windows activation” ya yi ta hanyar amfani da bayanin da na kawo a mataki na huɗu (4), ta nan ne zai nuna ma cewar yanzu fa ya zama “Activated”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter danna nan

    Domin karanta bayani akan Kafar Sadarwa ta WhatsApp: Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa ta WhatsApp danna nan

  • Mece Ce Kwamfuta?

    Mece Ce Kwamfuta?

    Kwamfuta – Kwamfuta wata na’urar wutar lantarki ce [electronic divice]; wacce take yin aiki a sakamakon waɗansu umarni da aka ajiye a cikin ɗakin ajiyarta [memory].

    Da za ta iya karɓar

    saƙon data [input], sai ta sarrafa wannan saƙon kamar yadda aka umarce ta [process].

    Sannan ta fitar da sakamako [output], sannan ta ajiye wannan sakamako domin amfani a nan gaba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mene Ne Data Da Information? danna nan.

  • Yadda Za Ka Yi Amfani Da Keyboard Ɗinka A Matsayin Mouse

    Yadda Za Ka Yi Amfani Da Keyboard Ɗinka A Matsayin Mouse

    Sau da yawa wasu sukan samu matsala da manunin kwamfutarnsu, wato “mouse”

    To daga lokacin da mouse ɗinka ya daina, a lokacin da za ka yi amfani da shi, to sai ka mayar da keyboard ɗinka ya zama kana iya aiki biyu da shi, ya yi aikinsa na keyboard sannan ya yi kuma na mouse.

    Yadda za a yi kuwa shi ne abi waɗanann matakan:

    • Sai ka yi amfani da Alt+Shift na hannun hagu +number lock sannan a danna Enter Key.
    • Sai a yi amfani da lambobi don gabatar da aikinka misali;

    Danna lamba 5 Yana matsayin Click

    Ko ka danna alamar + Yana matsayin Double click

    Ko kuma ka danna alamar – Yana matsayin Right click

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata danna koren rubutun nan