Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp

    Yadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp

    Yadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing A Waya.

    Mafi yawancin mutane suna yawan tambaya ta cewar sun ga abu a status na wani ya sanya a whatsapp, kuma suna da buƙata, amma ba yadda za su yi, gashi kuma suna so, har a wasu lokuta sukan nemi da wanda ya sanya wannan status da ya turo masu amma ya ƙi , to ta wannan Manhaja (Application) za ka iya amfani da shi wajen ɗaukar dukkanin wani nau’in abu da wani ya sanya a status na shi ba tare da ka buƙaci ya turo maka ba.

    Yadda masarrafin yake kuwa shi ne, ka shiga kasuwar hada-hadar masarrafai ta duniya wato Google Play Store ka nemi Status Saver, sai ka sauke shi a kan wayarka, sai ka sanya shi, ma’ana ka yi Installing na shi, da zarar ka yi, sai ka buɗe shi, zai ba ka dama ganin ɓangare guda biyu, na farko images, ma’ana hotuna da kuma Videos wato hoto mai motsi, anan ne za ka ga wajen images ya buɗe maka hotuna daban-daban, duk wanda kake da buƙatar ɗauka sai ka danne kan hoton, zai ba ka alamar memory card daga sama inda da zarar ka danna kansa shi kenan, sai ka je ka duba Gallery naka, za ka ga hoton a ciki, haka kuma wannan hanyar ake amfani da ita wajen ɗaukar video ma, idan kuma za ka ɗauke su ne duka, sai ka riƙa hawa kan hoton ko video kana zaɓa da zarar ka gama sai ka zaɓi memory card, zai nuna maka sun zauna a kai.

    Sannan idan ba so kake ka ajiye ba, akwai inda zai ba ka damar ka yi sharing a duk inda kake so, domin tura wa wani ko da kuwa kai ba ka ajiye shi a kan waya ko computer naka ba. Haka kuma akwai inda zai ba ka damar ka zaɓe su duka ta hanayar zaɓen guda ɗaya, sai wannan alamar ta fito, da zarar ka danna zai nuna ka zaɓe su duka, sai ka ajiye. Idan kuma gogewa za a yi, akwai alamar gogewa sai ka danna kan alamar zai zama ka goge hotunan ko video duka daga kan STATUS SAVER ɗin .

    Yadda Ake Amfani Da Shi A Taƙaice

    1. Ka zabi irin nau’in status da kake son ɗaukar hoto ko bidiyo.
    2. Sai ka dannan kan alamar saving domin ajewa.
    3. Da zarar ka aje, sai ka je cikin gallery ka duba.
    4. Za ka iya ajiye duka hotunan ko bidiyon ta hanyar zaɓar hotunan duka.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan.

  • Waƙa A Matsayin Sana’a

    Waƙa A Matsayin Sana’a

    Mawaƙa da dama sun dogara da yin waƙa wanda rayuwarsu ta dogara a kai; wannan tunani kuwa tun daga mawaƙan jiya har zuwa na yau waɗanda ake kiransu da Mawaƙan Situdiyo.

    Misali, Marigayi Alhaji (Dk.) Mamman Shata Katsina ya faɗi haka, a inda ya ce:

    Jagora: Ko ni Alhaji Sarkin waƙa,
    In nai waƙa kyakkyawa,
    Na samu kuɗi mai kauri,
    Na tara har sun kauri,
    Ba ashararu ba sakarci,
    Sai in kashe su ta hanya mai kyau.
    (Waƙar Kuɗi a kashe su ta hanya mai kyau).

    Kamilu Almajirin Maiwaƙa ma, ya bayyana haka a wata waƙarsa da yake cewa:
    Jagora: Waƙa nake yi domin na samu abin miya.
    (Waƙar Baba na Mashina).

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan

  • Yadda Ake (Recording) Ɗaukar Videon Abin Da Ake Gabatarwa A Fuskar Kwamfutarka Mai Ɗauke Da Windows

    Yadda Ake (Recording) Ɗaukar Videon Abin Da Ake Gabatarwa A Fuskar Kwamfutarka Mai Ɗauke Da Windows

    Recording – Shin kana da aboki wanda yake ɗauke da computer mai amfani da Windows 8, kuma yake shan wahalar aiki da sababbin al’amuran da ya zo da shi ? 

    Recording – Hanya mafi sauƙi da za ka taimake shi ita ce, ka samar masa da video tutorials a maimakon ɓata dogon lokaci wajen yin bayanin abubuwan.

    Capture Studio, wannan wani masarrafi ne dake aiwatar da wannan aiki. Ga hanyoyin da za a bi.

    Wanann masarrafin ba wai ɗaukar hoto mai motsi yake yi ba kaɗai.

    Haka kuma, za ka iya gyara bidiyon domin samun damar ɗaukar abin da ake yi a fuskar computer.

    Waɗannan bayanai guda biyar za su taimaka wajen gabatar da wanann aiki.

    Ɗauko Wannan Masarrafin Na Movavi Screen Recording Software

    Da fari, download ɗauko wannan masarrafin, sai ka sanya masarrafin Movavi’s screen recorder a kan Windows 8. A kula, lokacin da kasanya setup program ɗin , to ka canja kwamfutarka zuwa tsarin desktop.

    Wanda sanya wannan abin zai ɗauke ka wasu ƴan lokuta, sai ka bi bayanan da suke ba ka.

    Bayan ka gama sanyawa, masarrafin zai buɗe da kansa (sai dai in kaki ba shi damar ya bude da kansa wajen shigar da shi).

    Canja Tsarin Saite-saite

    Canja tsarin ɗaukar ya zama manual.

    Ko ka zaɓi abin da ka ga ya fi dacewa da kai daga cikin jerin sunayen Select Capture Area. Sai ka zaɓi sautin da ya yi maka: 

    Haka kuma, za ka iya ɗaukar sauti daga maɗaukar sauti, ma’ana microphone naka (ko kuma wani abu daban), ko kuma daga speaker mafitar sautin da ka ga ya dace.

    Sai ka duba alamar maɗaukar sautin (icon). Wannan ita ce kyakykyawar hanyar da ya kamata ka yi screencast yadda zai zama mai ɗaukar hankali, sai ka zaɓa ta hanyar danna manuninka (mouse cursor).

    Idan madaukar ya yi alamar ɗaurawa (yellow), wannan shi yake nuna madaukarka ta saitu).

    Dauki Abin Da Kake Aiwatarwa

    Da zarar ka bi duk hanyoyin dake sama ka ɗauki hanyar ɗaukar abin da kake aiwatarwa a fuskar computer naka.

    Sai ka danna kan REC ko kuma ka dannan F10 a kan keyboard, sai kawai ya fara ɗaukar abin da kake aiwatarwa a kan fuskar computerka. Sai ka danna madannin Windows key domin hanzartawa zuwa fuskar computer naka, idan kana son haka.

    Bayan ka ɗauki duk wani abu da kake aiwatarwa sai ka danna F10 domin tsayar da abin da kake ɗauka . Computer naka za ta koma kan tsarin desktop mode.

    Sai wani guri ya buɗe da ƙamshi domin ya ba ka damar ka yi yadda za ka yi da abin da ka ɗauka : sai ka ajiye shi a inda kake so a computer naka, ko ka turawa wani ko kuma ka yi amfani da abun gyara bideyon domin gyara shi yadda kake so.

    Gyaran Bidiyon Da Aka Ɗauka (Optional)

    Sai ka danna kan Edit zai ɗauke ka zuwa inda za ka yi gyaran bidiyon daka dauka a kan Movavi Video Editor program.

    Wanda da zarar ka yi haka, zai tafi da kansa zuwa wajen, to za ka iya gyara shi yadda kake so, misali kana son ka datsa shi trim, split zuwa gida-gida.

    Ko kuma sanya transitions a tsakanin kowannne yanki na bidiyon ka, ko kuma ka sanya music da kuma rubuce-rubuce titles, ko sanya abubuwa na musamman apply special effects, da dai sauran su.

    Idan ka gama gyaran, sai ka dannan kan Export sai ka zaɓi yadda kake son ka yi da bidiyon ko ka ajiye a kan computer naka ko ka yi rarraba shi (share) a yanar gizo domin ya amfanar.

    Ajiye Bidio

    Idan ba ka son ka gyara bidiyon, za ka iya tsallake mataki na hudu (4) sai kawai ka ajiye ko ka tura shi zuwa yanar gizo damin a amfana, ko ka ajiye shi kawai a kan computer naka.

    Shi wannan masarrafin na The Movavi screen recording software ana san ya shi akan kowanne irin nau’in computer, kuma ka tabbatar ka ajiye shi, a inda idan ka tashi neman sa nan gaba, ko kayi (uploading) dorashi a yanar gizo.

    za ka iya bincika wanna adireshin domin samu wannan bayani da yaren turanci, shine a matsayin matsotsar Ilimi, wato (reference).
    http://www.movavi.com/support/how-to/how-to-record-windows8.html©Movavi.com

    Haka kuma domin ɗauko wannan masarrafi za ka iya dann kan wannan rubutun mai ruwan bula, (blue)…….. download.

    Domin Karanta Cikakken Bayani A kan Yadda Ake Tsayar Da Update Na Windows 8 Da Kuma 10 danna nan

    Domin karanta bayani akan Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta? danna nan

  • Yadda Ake Macaroni 2

    Yadda Ake Macaroni 2

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Macaroni su ne:

    • Albasa
    • Tumatir
    • Green beans (koren wake)
    • Potatoes (dankali)
    • Niƙaƙƙen nama
    • Abin ɗanɗano
    • Vinegar (khal)
    • Kasbara
    • Shammar

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Tukunya
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Ludayi
    • Abin daka
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami albasa, tumatir, koren wake, duk a yi slicing ɗin su, sai a yanka dankali ƙanana, a soya sai a ajiye shi a gefe; sai a sa mai daidai ƙima a tukunya, ki zuba minced meat (niƙaƙƙen nama) a ciki, a soya kar ya yi ƙarau, a zuba albasa da tumatir a ci gaba da juyawa. Sai a soya green beans da ɗan mai kaɗan, in miyar ta dahu a zuba abin ɗanɗano a zuba dankalin, a sa shammar da kasbara ta ƙara dahuwa kaɗan sai a sauke a ci da macaroni fara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Shinkafa Mai Ƙwai danna nan

    Dominn karanta bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan

  • Yadda Ake Haɗa Man Gashi

    Yadda Ake Haɗa Man Gashi

    Idan aka ce man gashi, ana nufin mai da muke amfani da shi wajen kula da gashin kanmu ko mace ko namiji.

    Mukan yi amfani da man gashi domin ƙayatar da shi wajen saka shi; laushi, ƙamshi, hana ƙuraje da ƙyasbi da kwarkwata samun guri a zama gashin, sannan kuma domin gashi ya ƙara tsayi da cika.

    Sinadaran Haɗin Su Ne:

    • Petroleum jelly wato Vasseline
    • Paffarin oil
    • Palm kennel oil wato baƙin man kwakwa
    • Candle Wax wato candir
    • Menthol
    • Colour wato kala
    • Sai turaren haɗin

    Amfanin Ko Wani Sinadarin Haɗin Man Gashin

    • Petroleum jelly shi ne kamar Vasseline amma ba shi da maiƙo
    • Paraffin oil shi yake saka haɗin maiƙo
    • Palm kennel shi yake ƙara tsawon gashi
    • Candle wax shi yake ba wa haɗin damar daskarewa bayan an gama
    • Menthol shi yake taimakawa wajen kashe dandruff (ƙyasbi) da saura ƙurajen kai
    • kala shi yake canja launin man
    • Sai turare shi yake saka man gashin ya yi ƙamshi

    Duka waɗannan sinadaran sanannu ne a kasuwa, sannan farashinsu na da arha gwargwadon adadin da ake buƙata. Wajen wannan haɗi, a tabbatar da bin ƙa’idoji domin samun sakamakon da ake da buƙata

    Kayan Amfani Wajen Haɗin Man Gashi

    • Gas cooker/Murhu/Risho
    • Tukunya madaidaiciya.
    • Babban cokali ko ludayi domin motsa haɗin man gashin.
    • Robobin man gashi da za a juye man bayan an kammala haɗin.

    Yanda Ake Haɗin Man Gashi

    • Da farko za a ɗauko tukunya a ɗora ta a kan risho ko gas cooker bayan an kunna,
    • Sai a juye petroleum jelly ɗin a cikin tukunyar, a dinga juyawa da cokali ko ludayi
    • Sannan a ɗauko candle wax a saka, shi ma a cikin tukunyar bayan petroleum jelly ya gama narkewa a ci gaba da juyawa da cokali, har ya narke gaba ɗaya.
    • Sai a ɗauko parrafin oil da palm kennel oil, a juye su tare a cikin tukunyar, a ci gaba da motsawa da cokali.
    • Daga nan, sai a kashe wutar, a sauke tukunyar,
    • ana sauke tukunyar sai a gaggauta zuba kala a cikin tukunyar haɗin, a motsa shi da kyau.
    • Bayan minti uku Sai a zuba turaren haɗin
    • Sannan a kawo Menthol ɗin shi ma a zuba a cikin haɗin, a ci gaba da motsawa.
    • Sannan a bar haɗin ya kai a kalla minti goma sannan a zuzzuba robobin man gashin.
    • Daga nan kuma sai a bar su a buɗe su sha iska, domin man ya daskare. Shi kenan man gashinmu ya kammala.

    Gargaɗi

    Wajen wannan haɗin a tabbatar da cewa an tanadi kayan haɗi da sinadaran haɗin da ya kamata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sabulun Wanka danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

  • Yadda Ake Gima Macaroni Jallof

    Yadda Ake Gima Macaroni Jallof

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Gima Macaroni Jallof su ne:

    • Niƙaƙƙen nama/mai
    • Kayan miya
    • Tafarnuwa
    • Masoro
    • Girfa
    • Shammar
    • Abin ɗanɗano

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Tukunya
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Ludayi
    • Abin daka
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗa Macaroni Jallof

    Za a samu tukunya a zuba mai daidai yawan girkin, a sa naman a ciki, a soya sama-sama a zuba mai kaɗan a daka garlic da sauran kayan ƙamshi, a zuba abi ɗanɗano a jefa girfa. Idan ya soyu, a ƙara ruwa kaɗan a ciki.

    A gefe kuma a dafa farar macaroni daban, kar ta dafe. Idan ta dahu sama-sama, a tace a wanke ta da ruwan sanyi sai a zuba a cikin tukunyar kayan miya, a sa ludayi a juya a hankali, har ta haɗe jikinta

    a rufe ta, ta turara kamar minti 3, a sauke

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Macaroni 2 danna nan.

  • Yadda Ake Fanke

    Yadda Ake Fanke

    Fanke wani abinci ne da ake yin sa da fulawa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Fanke Su Ne:

    • Fulawa
    • Sugar
    • Gishiri
    • Yist
    • Ruwa
    • Mai (na suya)

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Cokali

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami fulawa a ɗan zuba gishiri a ciki da yiest a sa ruwa a kwaɓa shi daidai yadda ake buƙata.

    Sai a haɗa a buga shi daidai misali, a saka a rana ya tashi a soya, har sai ya yi ruwan ƙasa mai haske.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Dale danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda AkeTherapeutic Food (abincin yara) danna nan

  • Yadda Ake Alala

    Yadda Ake Alala

    Alala wani abinci ne, da ake yin sa da wake. Ana iya sakawa a leda ko kuma gwangwani.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Alala su ne:

    • Wake
    • Manja
    • Maggi
    • Albasa
    • Kifi
    • Ƙwai
    • Attaruhu

    Kayan Aiki

    • Turmi da Taɓarya
    • Murhu/Risho/Gas
    • Kasko
    • mazubi (mai tsafta)
    • wuƙa
    • Cokali
    • Ledoji

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami wake a surfa shi a wanke shi a zuba masa kayan miya ban da tumatir, a markaɗo shi, a juye shi a babban kwano;

    Sai a saka maggi, gishiri, kifi, ƙwai, a saka ruwan ɗumi, sai a juya shi yadda ake so, sai a zuba mata manja;

    Ki daɗa juyawa. Daga nan a zuba ta a cikin ledoji ko kuma gwangwani, a sa a ruwa ya tafasa har sai ta dahu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Fanke danna nan.

  • Yadda Ake Mahshi

    Yadda Ake Mahshi

    Mahshi wani abinci ne da ake haɗawa da shinkafa, kayan lambu da kuma nama.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Mahshi

    • Gatafosa/ yalon bature (garden egg)
    • Potatoes
    • Onions
    • Nama
    • Shinkafa

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kwano
    • Cokali
    • Wuƙa
    • Kasko

    Yadda Ake Haɗawa

    A sami waɗannan sinadaran da aka lissafo a sama, kifafe cikinsu, dukkan su, su yi falai-falai; amma ba a yanka suba, za ki dafa shinkafa ta dahu kaɗan, sai ki kwashe ki saka a cikin kwano.

    Idan ta yi sanyi, ki kawo niƙaƙƙen nama, ki zuba naman ya fi shinkafar yawa, sai a zuba shammar da kasbara ki yayyanka su da tafarnuwa da gishiri da maggi ki chakuɗa ya haɗe jikinsa.

    Sai ki wanke kayan da kika fafe, ki tsane ruwansu, ki wanke koren tattasai sai (black pepper) ki zuba a cikin haɗin; ki dinga ɗiban shinkafar da kika haɗa, kina zubawa a cikin kayan da kika fafe; ki rinƙa soyawa kaɗan-kaɗan idan kin gama sai ki saka a cikin dage-dagen tumatir irin wanda ake ci da kufta.

    Domin karanta Yadda Ake Kebab (V.I.P SOUP) danna nan

  • Yadda Ake Fish Soup

    Yadda Ake Fish Soup

    Fish Soup wata miya ce da ake yi da kifi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Fish Soup su ne:

    • Fish (kifi)
    • Maggi, salt (Abin ɗanɗano, gishiri)
    • Curry
    • Oil
    • Kayan miya
    • Kanwa

    Kayan Aiki

    • Murhu/Risho/Gas
    • Kasko
    • Mazubi (mai tsafta)
    • Wuƙa

    Yadda Ake Haɗawa

    Da farko a soya mai da albasa, a zuba yankakken tattasai da tumatir da albasa a kawo ruwa kaɗan a zuba da ‘yar kanwa;

    A gyara kifin a wanke a zuba, a saka gishri da maggi da ƙiƙanshi kamar minti goma;

    Sai a sauke kana iyaci da shinkafa ko cous – cous e.t.c.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Alala danna nan